Rayo tana yi wa Barcelona tauri a La Liga

An wallafa

Rayo Vallecano ta karbi bakuncin Barcelona, domin buga wasan mako na 31 a La Liga ranar Laraba a Estadio Teresa Rivero.

Barcelona tana matakin farko a kan teburin La Liga da maki 76, ita kuwa Rayo mai maki 40 tana ta 10 a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Bayan da Barca ta ci Rayo wasa 13 a jere har da karawa biyar da take cin kwallo biyar ko fiye da hakan a baya, yanzu batun ya sauya da kyar take kwatar kai.

Domin Barcelona ta kasa cin Rayo a karawa uku baya da suka yi har da kasa zura kwallo a raga.

A wasan farko a bana da suka buga da fara La Liga sun tashi 0-0 ranar 13 ga watan Agusta a Camp Nou.

Ko a kakar bara ta 2021/22 Rayo ce ta doke Barcelona gida da waje kowanne da cin 1-0.

Frenkie de Jong da Pedri sun koma yi wa Barca tamaula, bayan jinya - kawo yanzu masu jinya sun hada da Ousmane Dembele da Andreas Christensen da kuma Sergi Roberto.

To sai dai kyaftin Sergio Busquets ya karbi katin gargadi na biyar a wasa da Atletico a karshen mako, ba zai yi karawa da Rayo ba.

Cikin 'yan wasa 21 da Xavi zai fuskanci Rayo da ya sanar har da matasan kungiyar da suka hada da Pablo Torre da Chadi Riad da Arnau Tenas da kuma Lamine Yamal.

A bangaren mai masaukin baki kuwa, Radamel Falcao ba zai yi wa Rayo wasan ba, wanda ke jinyar mako uku nan gaba.

Shin ko kun san?

Wasan da Rayo ta ci Barcelona 1-0 a karawar farko a La Liga a bara a cikin Oktoban 2021 ranar Laraba ce.

Idan ba a ci Barca kwallo ba za ta kafa tarihin karawa 24 a kaka ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba.

Haka kuma Barcelon na bukatar cin karawa daya domin kafa tarihin yawan cin wasanni a kaka a La Liga.