Za a buga wasa na 31 tsakanin Ingila da Faransa na uku a Kofin Duniya

England vs France

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Tawagar Ingila za ta kara da ta Faransa a wasan daf da na kusa da na karshe a Gasar Kofin Duniya a Qatar ranar Asabar.

Ingila mai Kofin Duniya da ta dauka a 1966 ta kawo wannan matakin, bayan da ta ja ragamar rukuni na biyu da maki bakwai mai dauke da Wales da Amurka da kuma Iran.

Faransa ce ta fara kai wa zagaye na biyu a Qatar, bayan da ta ja ragamar rukuni na hudu da maki shida mai dauke da Australia da Tunisia da kuma Denmark.

A zagaye na biyu ne Faransa ta doke Poland 3-1 ranar Lahadi.

Wannan shi ne karon farko da za su kara a zagayen ziri daya kwale a gasar tamaula, kuma na farko a Kofin Duniya tun 1982.

Sai dai karo na 31 da za su kece raini a tsakaninsu na uku a Kofin Duniya, inda Ingila ta yi nasara a 16 da canjaras biyar, Faransa ta ci karawa tara.

Za a buga wasan tsakanin Kyalin Mbappe mai kwallo biyar a raga mai takarar takalmin zinare da Jude Bellingham, matashin da yake haskawa a Qatar.

Tawagar Ingila ta zura kwallo 12 a raga kawo yanzu, ita kuwa Faransa ta ci tara, saboda haka ana sa ran za a ci kwallaye da yawa idan an bude karawar ba tasre gida.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Faransa ce mai rike da Kofin Duniya, wanda ta lashe a Rasha a 2018, kuma na biyu jumulla da ta dauka.

Wasannin da aka kara tsakanin Ingila da Faransa:

Wasan sada zumunta     13 ga watan Yunin 2017

  • France 3 - 2     England          

Wasan sada zumunta     17 ga watan Nuwambar 2015          

  • England           2 - 0     France

Gasar Nahiyar Turai         11 ga watan Yunin 2012          

  • France 1 - 1     England          

Wasan sada zumunta      17 ga watan Nuwambar 2010         

  • England           1 - 2     France

Wasan sada zumunta      26 ga watan Maris 2008         

  • France 1 - 0     England          

Gasar Nahiyar Turai           13 ga watan Yunin 2004

  • France 2 - 1     England          

Wasan sada zumunta      2 ga watan Satumbar 2000

  • France 1 - 1     England          

Wasan sada zumunta      10 ga watan Fabrairun 1999          

  • England           0 - 2     France

Wasan sada zumunta      7 ga watan Yunin 1997

  • France 0 - 1     England          

Gasar Nahiyar Turai           14 ga watan Yunin 1992

  • England           0 - 0     France

Wasan sada zumunta      19 ga watan Fabrairun 1992          

  • England           2 - 0     France

Wasan sada zumunta      29 ga watan Fabrairun 1984          

  • France 2 - 0     England          

Gasar Kofin Duniya    16 ga watan Yunin 1982          

  • England           3 - 1     France

Wasan sada zumunta      12 ga watan Maris 1969         

  • England           5 - 0     France

Gasar Kofin Duniya   20 ga watan Yulin 1966

  • England           2 - 0     France

Gasar Nahiyar Turai          27 ga watan Fabrairun 1963          

  • France 5 - 2     England          

Gasar Nahiyar Turai         3 ga watan Octoban 1962          

  • England           1 - 1     France

Wasan sada zumunta      27 ga watan Nuwambar 1957         

  • England           4 - 0     France

Wasan sada zumunta      15 ga watan Mayun 1955          

  • France 1 - 0     England          

Wasan sada zumunta      3 ga watan Octoban 1951          

  • England           2 - 2     France

Wasan sada zumunta      22 ga watan Mayun 1949          

  • France 1 - 3     England          

Wasan sada zumunta      3 ga watan Mayun 1947          

  • England           3 - 0     France

Wasan sada zumunta      26 ga watan Mayun 1938          

  • France 2 - 4     England          

Wasan sada zumunta      14 ga watan Mayun 1931          

  • France 5 - 2     England          

Wasan sada zumunta      9 ga watan Mayun 1929          

  • France 1 - 4     England          

Wasan sada zumunta      17 ga watan Mayun 1928          

  • France 1 - 5     England          

Wasan sada zumunta      26 ga watan Mayun 1927          

  • France 0 - 6     England          

Wasan sada zumunta      21 ga watan Mayun 1925          

  • France 2 - 3     England          

Wasan sada zumunta      17 ga watan Mayun 1924          

  • France 1 - 3     England          

Wasan sada zumunta  10 ga watan Mayun 1923          

  • France 1 - 4     England