Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a buga wasa na 31 tsakanin Ingila da Faransa na uku a Kofin Duniya
Tawagar Ingila za ta kara da ta Faransa a wasan daf da na kusa da na karshe a Gasar Kofin Duniya a Qatar ranar Asabar.
Ingila mai Kofin Duniya da ta dauka a 1966 ta kawo wannan matakin, bayan da ta ja ragamar rukuni na biyu da maki bakwai mai dauke da Wales da Amurka da kuma Iran.
Faransa ce ta fara kai wa zagaye na biyu a Qatar, bayan da ta ja ragamar rukuni na hudu da maki shida mai dauke da Australia da Tunisia da kuma Denmark.
A zagaye na biyu ne Faransa ta doke Poland 3-1 ranar Lahadi.
Wannan shi ne karon farko da za su kara a zagayen ziri daya kwale a gasar tamaula, kuma na farko a Kofin Duniya tun 1982.
Sai dai karo na 31 da za su kece raini a tsakaninsu na uku a Kofin Duniya, inda Ingila ta yi nasara a 16 da canjaras biyar, Faransa ta ci karawa tara.
Za a buga wasan tsakanin Kyalin Mbappe mai kwallo biyar a raga mai takarar takalmin zinare da Jude Bellingham, matashin da yake haskawa a Qatar.
Tawagar Ingila ta zura kwallo 12 a raga kawo yanzu, ita kuwa Faransa ta ci tara, saboda haka ana sa ran za a ci kwallaye da yawa idan an bude karawar ba tasre gida.
Faransa ce mai rike da Kofin Duniya, wanda ta lashe a Rasha a 2018, kuma na biyu jumulla da ta dauka.
Wasannin da aka kara tsakanin Ingila da Faransa:
Wasan sada zumunta 13 ga watan Yunin 2017
- France 3 - 2 England
Wasan sada zumunta 17 ga watan Nuwambar 2015
- England 2 - 0 France
Gasar Nahiyar Turai 11 ga watan Yunin 2012
- France 1 - 1 England
Wasan sada zumunta 17 ga watan Nuwambar 2010
- England 1 - 2 France
Wasan sada zumunta 26 ga watan Maris 2008
- France 1 - 0 England
Gasar Nahiyar Turai 13 ga watan Yunin 2004
- France 2 - 1 England
Wasan sada zumunta 2 ga watan Satumbar 2000
- France 1 - 1 England
Wasan sada zumunta 10 ga watan Fabrairun 1999
- England 0 - 2 France
Wasan sada zumunta 7 ga watan Yunin 1997
- France 0 - 1 England
Gasar Nahiyar Turai 14 ga watan Yunin 1992
- England 0 - 0 France
Wasan sada zumunta 19 ga watan Fabrairun 1992
- England 2 - 0 France
Wasan sada zumunta 29 ga watan Fabrairun 1984
- France 2 - 0 England
Gasar Kofin Duniya 16 ga watan Yunin 1982
- England 3 - 1 France
Wasan sada zumunta 12 ga watan Maris 1969
- England 5 - 0 France
Gasar Kofin Duniya 20 ga watan Yulin 1966
- England 2 - 0 France
Gasar Nahiyar Turai 27 ga watan Fabrairun 1963
- France 5 - 2 England
Gasar Nahiyar Turai 3 ga watan Octoban 1962
- England 1 - 1 France
Wasan sada zumunta 27 ga watan Nuwambar 1957
- England 4 - 0 France
Wasan sada zumunta 15 ga watan Mayun 1955
- France 1 - 0 England
Wasan sada zumunta 3 ga watan Octoban 1951
- England 2 - 2 France
Wasan sada zumunta 22 ga watan Mayun 1949
- France 1 - 3 England
Wasan sada zumunta 3 ga watan Mayun 1947
- England 3 - 0 France
Wasan sada zumunta 26 ga watan Mayun 1938
- France 2 - 4 England
Wasan sada zumunta 14 ga watan Mayun 1931
- France 5 - 2 England
Wasan sada zumunta 9 ga watan Mayun 1929
- France 1 - 4 England
Wasan sada zumunta 17 ga watan Mayun 1928
- France 1 - 5 England
Wasan sada zumunta 26 ga watan Mayun 1927
- France 0 - 6 England
Wasan sada zumunta 21 ga watan Mayun 1925
- France 2 - 3 England
Wasan sada zumunta 17 ga watan Mayun 1924
- France 1 - 3 England
Wasan sada zumunta 10 ga watan Mayun 1923
- France 1 - 4 England