Yadda ya kamata ku motsa jiki a lokacin azumi

Asalin hoton, Getty Images
Yin azumi na nufin dole mutum ya yi tunanin tsara yadda zai riƙa motsa jikinsa saboda shi kansa jikin ya canja yadda yake aiki.
Wannan ne abin da mai horar da motsa jikin Belal Hafeez da masanin cimaka, Nazima Qureshi suka fayyace. Mata da mijin sun rubuta littafi mai suna Healthy Ramadan Guide kan yadda mutum zai tsara cimakansa da motsa jiki a lokacin azumi.
"An fi buƙatar mutum ya ninka ibadunsa da addu'o'i da kusanci ga Allah ne a azumi. Abubuwan da muka ci da yadda muka motsa jiki za su taimaka wajen cika wannan burin domin suna da rawar da za su taka wajen rage gajiya, da tsara aikace-aikace," in ji Hafeez.
Idan kana so ka kasance cikin ƙoshin lafiya a kwana 30 na azumin, ga wasu abubuwan da za ku kiyaye.
Shan ruwa

Asalin hoton, Getty Images
"Mutane da dama suna gane cewa suna da ciwon kai a ranakun farkon Ramadan - wanda bai rasa nasaba da rashin isasshen ruwa a jiki, in ji Qureshi.
"Kamata ya yi mutum ya sha tamkar ba ya azumi. Don haka sai mutum ya tsara shan ruwa tsakanin lokacin sahur da buɗa-baki. Yadda ya kamata shi ne a sha lita ɗaya da sahur."
Idan kuma kana shan lemuka masu ɗauke da sinadarin caffein da rana, shan ruwan sai ya ƙara muhimmanci saboda daina shan lemukan masu caffeine ma yana jawo ciwon kai.
"Abu mai muhimmanci shi ne a rage shan lemuka masu caffeine kafin Ramadan," in ji Qureshi.
Kyakkyawan shiri

Asalin hoton, Getty Images
"Saboda abinci biyu za ka ci maimakon uku - buɗa-baki da yamma da sahur da asuba - ya kamata ka zaɓi abincin da zai ba jikin ƙarfi sosai," in ji Hafeez.
"Wasu na tunanin saboda jikinsu ba ƙarfi za su kwanta ne kawai su yi barci ba tare da sun tashi sun yi sahur ba. Ba daidai ba ne.
"Ya kamata abincin sahur ɗin ya ƙunshi sinadarin carbohydrates da na protein da maiƙo, sannan idan da hali a samu ƴaƴan itace a haɗa.
"Da daddare kuma oats yana cikin abubuwan da muke bayar da shawara a ci saboda yana ɗauke da muhimman sinadarai. Bayan hatsin oats, ina shan madarar greek da tsabar chia saboda yana ɗauke da maiƙo, sai kuma ƴaƴan itatuwa."
Ka guji cin abinci mai yawa lokacin buɗe-baki
Domin ba ka ci abinci ba da rana baki ɗaya, wata zuciyar za ta riƙa raya maka 'ka biya bashin' abin da ba ka ci ba, musamman idan kana buɗa-bakin ne tare da ƴanuwa da abokai, in ji Hafeez.
"Misali shi ne samosa. Kowane yana ɗauke da calory 250, kuma ba a cin ɗaya kawai - an fi cin biyu zuwa uku a farkon cin abinci. Wannan na nufin za ka iya cike gurbin ƙarfin jikin da ka ke buƙata wato energy tun a samosa.
"Idan sau ɗaya kake yin haka a mako, babu laifi sosai. Amma idan ya zama kullum, zai zama kana cin abinci ne sama da wanda ba ya azumin."
Qureshi ya ƙara da cewa, "abin da muke da ba da shawarawa shi ne idan ka yi buɗa-baki, ka fara da ruwa da dabino da wasu ƴaƴan itatuwa, sai ka tafi sallah kafin ka ci abinci bayan sallah. Ka riƙa haɗawa da abincin gargajiya, amma ka tabbatar suna ɗauke da sinadaran protein, waɗanda aka hada a cikin miya ko kaza ko kifi ko tsire."
Ka daidaita cimaka

Asalin hoton, Getty Images
Idan kana cin abinci tare da wasu ne - kamar a cikin ƴanuwa ko abokai - akwai tunanin cin duk abin da aka kawo, amma akwai yadda ya kamata a yi.
Hafeez ya ce, "babban abin da muke bayyana wa mutane shi ne su riƙa bi a hankali wajen cin abinci. A riƙa jan ƙafa, ana ci ana hira. Idan baƙinka suka lura cewa ka cinye naka, alhalin kowa yana cin abinci, za a nemi ka ƙara. Don haka ka bi a hankali."
Idan ma'auratan nan biyu za su halarci taron da wani shirya, suna zuwa da wani abincin da suka yi amannar zai kara wa abincin inganci.
Ka motsa jiki a lokacin da ya fi maka daɗi
"mutane da dama za su fita tattaki na awa ɗaya ko biyu kafin buɗa-baki, da zarar sun kammala sai su sha ruwa," in ji Hafeez.
"Amma idan wannan ba zai yi daidai da tsare-tsarenka ba, ka yi yadda kake so. A bara na ji daɗin fita tattaki ne da rana. Fita motsa jiki na farko yakan zo da ƙalubale, amma jiki yana sa saurin sabo da juriya."
"Sannan za ka iya motsa jikinka da za kammala buɗa-baki.
Ka mayar da hankali kan ƙarfin jiki da daidaito

Asalin hoton, Getty Images
Ba tare da la'akari da lokacin da za ka motsa jiki, yana da kyau ka tsara yadda jikinka zai saba.
"Ka rage yawan aikace-aikace a lokacin Ramadan," in ji Hafeez. "Ka yi amfani da watan wajen tsara cimaka da zirga-zirga da daidaito."
"Kuma yana da kyau ka riƙa samun barci mai kyau idan kana so jikinka ya samu sukuni.
Haka lokacin bai dace da zama lokacin fara zuwa motsa jiki a gym ba, in ji Hafeez. Ya ce zuwa tattaki ya fi.
Gyara tunaninka
Idan ƙarfin jikinka yana yin kaɗan a lokacin Ramadan, sai ka tunanin asalin dalilin yin azumin.
"Azumin ibada ne, wanda wannan ne abin da ya fi muhimmanci. Dole yana buƙatar juriya. Idan azumin yana ba ka wahala, sai ka tuna, ka ce ba matsala ai na kwana 30 ne kawai. A tunanina hakan zai ƙara wa mutum juriya."











