Mece ce gaskiyar iƙirarin Trump cewa Ukraine ce ta tsokani Rasha?

Shugaba Donald Trump ke zantawa da manema labarai a adarsa.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Matt Murphy & Jake Horton
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya zargi Ukraine da laifin yaƙin da ƙasar ke yi da Rasha, a wani furucin da ya yi daga gidansa na Mar-a-Lago da ke jihar Florida.

Yayin da yake zantawa da manema labarai, Trump ya kuma yi ikirarin cewa farin jinin shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ragu, sannan ya ce ya lura cewa har yanzu Ukraine ta kasa gudanar da zaɓen da aka tsara yi, sakamakon dokar soji da aka sanya a ƙasar.

Kalaman na Trump - waɗanda wasu daga cikinsu sun yi kama da batutuwan da Rasha ta saba magana game da yaƙin - na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan da jami'an Amurka suka gana da tawagar Rasha a Riyadh domin buɗe tattaunawar kawo ƙarshen rikicin da aka shafe kusan shekara uku ana gwabzawa.

Daga baya, Zelensky ya zargi Trump da yarda da ''labaran ƙarya'' da Rasha ta ƙirƙira.

Sashen tantance labarai na BBC, ya yi nazari kan iƙirarin na shugaba Trump.

Iƙirarin: 'Bai kamata ku fara shi ba'

Hukumomin Ukraine sun bayyana damuwa kan rashin sanya ƙasar cikin tattaunawar ranar Talata da aka yi a birnin Riyadh.

Amma Trump ya yi watsi da hakan, inda ya shaida wa manema labarai cewa Ukraine na da aƙalla shekara uku na kawo ƙarshen yaƙin, kafin daga baya ya zargi Kyiv da laifin fara yaƙin.

"Bai kamata ku fara shi ba," in ji shi. A baya Kremlin ta zargi Ukraine da fara yaƙi da Rasha.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Su suka fara yaƙin a 2014. Burinmu shi ne dakatar da yaƙin. kuma ba mu muka fara yaƙin a 2022 ba," kamar yadda shugaban Rasha, Vladimir Putin ya faɗa wa mai gabatar da shirin Tucker Carlson a Amurka a watan Fabrairu 2024.

Amma binciken BBC ya gano cewa ba Ukraine ce ta fara yaƙin ba. Rasha ce ta ƙaddamar da mayayar Ukraine a watan Fabrairun 2022, bayan ta ƙwace yankin Crimea a 2014.

Ƙwace Crimea na zuwa ne bayan hamɓarar da shugaban Ukraine mai samun goyon bayan Rasha ta hanyar jerin zanga-zanga.

Haka kuma Rasha ta goyi bayan wasu dakaru da ke faɗa da Ukraine waɗanda suka ƙwace yankunan gabashin ƙasar, sannan ta zargi gwamnatin kyiv da nuna wariya da kisan kiyashi ga masu magana da harshen Rashanci a ƙasar.

To sai dai kotun duniya ta musanta iƙirarin na Moscow.

Bayan rugujewar wasu yarjeniyoyin kawo ƙarshen rikicin da ya biyo bayan shekara ta 2014 - Rasha ta fara wani gagarumin aikin girke sojoji a kan iyakarta da Ukraine a ƙarshen shekarar 2021.

Putin ya ƙaddamar da farmakin ne a ranar 24 ga watan Fabrairun 2022, inda ya bayyana cewa, manufar wannan aiki shi ne "karkatar da sojoji da kuma hana" gwamnatin Volodymyr Zelensky da ke goyon bayan ƙasashen Yamma da kuma hana ƙasar shiga ƙungiyar Nato.

A zaɓen 'yan majalisar dokokin Ukraine na ƙarshe, goyon bayan 'yan takara masu ra'ayin riƙau ya kai kashi 2%. Har ila yau, ya kamata a lura cewa Zelensky Bayahude ne kuma an ɗauki jam'iyyarsa a matsayin mai matsakaicin ra'ayi.

Kuma yayin da jami'an Nato faɗa a 2021 cewa Ukraine ta kasance 'yar takara don shiga cikin ƙawancen ƙasashen yammacin Turai a nan gaba, ba ya cikin wani tsari na bin wata ƙa'ida a hukumance.

Iƙirarin: 'Bana son furtawa, amma farin jininsa ya ragu da kashi 4 cikin 100'

Shugaba Trumpo ya kuma yi ƙirarin cewa farin jinin Zelensky ya ragu da kashi huɗu cikin 100.

Sai ba a san da wane ma'auni shugaban ya dogara wajen iƙirarin nasa ba, saboda bai bayar da wata hujja ba. Mun tambayi fadar 'White House' ta tantance mana.

Wata ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da wata cibiyar nazarin zamantakewa ta Ukraine, mai mazauni a Birtaniya ta gudanar, ta nuna cewa kashi 57 cikin 100 na ƴanƙasar sun ce sun yarda da shugaban.

Sai dai hakan ya ragu daga kashi 77 cikin 100 da shugaban ke da shi a ƙarshen 2023, kuma kashi 90 a watan Mayun 2022, wani abu da ke nuna raguwar farin jinin shugaban.

Wasu ƙuri'un jin ra'ayin jama'ar, sun nuna cewa Zelensky zai kasance a bayan babban abokin hamayyarsa, tsohon shugaban sojojin ƙasar, Zaluzhnyi a zagayen farko na zaɓen ƙasar da ke tafe, lamarin da ke hasashen zuwa zagaye na biyu na zaɓen.

Gudanar da ƙuri'ar jin ra'ayin jama'ar a hukumance zai bayar da wahala, saboda miliyoyin ƴan Ukrane ne suka tsere wa ƙasar sannan Rasha ta mamaye kusan kashi ɗaya bisa biyar na ƙasar.

Janar Valerii Zaluzhnyi ka iya zama babban abokin hamayyar Shugaba Zelensky, idan ya tsaya zaɓen shugaban ƙasar na gaba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Janar Valerii Zaluzhnyi ka iya zama babban abokin hamayyar Shugaba Zelensky, idan ya tsaya zaɓen shugaban ƙasar na gaba.

Dangane da kalaman na Trump, wasu manyan kafafen yaɗa labaran ƙasar Rasha sun karɓi wannan ikirari tare da bayar da misali da wani ɗan majalisar dokokin Ukraine da mai sukar Zelensky, Oleksandr Dubinsky, suka yi a Telegram, wanda suka ce sun goyi bayan tantancewar da Trump ya yi.

An tuhumi Dubinsky da laifin cin amanar ƙasa a Ukraine, kuma ana zarginsa da "aiki bisa umarnin leƙen asirin Rasha" - abin da ya musanta.

Ikirari: 'An kasa gudanar da zaɓuka a Ukraine, kuma ana aiki da dokar soji'

Trump ya kuma ja hankali kan cewa Ukraine ba ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ba tun 2019, lokacin da Zelensky - wanda a baya ɗan wasan barkwanci ne maras tarihin siyasa - ya ɗare karagar mulki.

Wa'adin mulkinsa na farko na shekara biyar, ya kamata ya ƙare a ƙarshen Mayun 2024. To amma kasancewar ƙasar na ƙarƙashin dokar soji tun bayan mamayar Rasha a Fabrairun 2022- ya sa aka ɗage gudanar da zaɓukan.

A shekarar 2015 ne aka tsara dokokin yaƙi a Ukraine - jim kaɗan bayan Rasha ta mamaye yankin Crimea, kuma shekaru kafin Zelensky da jam'iyyarsa ta 'Servant of the People' su hau karagar mulki.

A watan Nuwamba dukkan jam'iyyu a majalisar dokokin ƙasar suka goyi bayan ɗage zaɓen har sai yaƙin ya ƙare, matsayin da wani bincike ya nuna cewa ya samu karɓuwa a wurin 'yan ƙasar ta Ukraine.

Kimanin kashi 60 cikin 100 na mutane ba sa goyon bayan gudanar da zaɓe, don maye gurbin Zelensky a lokacin yaƙin, a cewar wata ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da cibiyar Republican ta duniya ta gudanar a watan Satumba da Oktoba.

Zelensky ya sha alwashin gudanar da sabon zaɓe da zarar an kawo ƙarshen rikicin kuma har yanzu bai tabbatar da cewa yana da niyyar tsayawa takara ba.

Wasu ƙwararru sun ce gudanar da zaɓe a Ukraine kafin kawo ƙarshen rikici ba abu ne mai yiwuwa ba, saboda hare-haren da Rasha ke kai wa a birane da yawa kuma miliyoyin 'yan ƙasar ke gudun hijira a ƙasashen waje ko kuma suke zama ƙarƙashin mamayar Rasha.

Shigar da Trump ya yi kan wannan batu na zuwa ne sa'o'i bayan da fadar Kremlin ta nuna shakku kan sahihancin Zelensky yayin da wa'adinsa ya kare, ikirarin da Moscow ta sha yi a watannin da suka gabata.

A ranar 28 ga watan Janairu, Putin ya kira Zelensky "haramtaccen shugaba" a wata hira da ya yi da kafofin yada labaran Rasha.

Dangane da yanayin zaɓen, Trump ya ce yana sane da cewa ana yawan zargin Rasha, ''Wannan ba abu ne na Rasha ba, wani abu ne ya fito daga gare ni, daga wasu ƙasashe."

A nasa bangaren, Zelensky a baya ya ce zai zama "rashin hankali ne a ɓullo da batun zaɓe" a wannan lokaci na tsakiyar rikici.

Ƙarin rahoto daga BBC Monitoring.