Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta sha kashi a gidan Bournemouth da ci 2-0
Bournemouth ta caskara Arsenal da ci 2-0 a wasan Pemeir League mako na takwas a filin wasa na Vitality, inda Arsenal ta ƙare wasan da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da alƙalin wasa ya bai wa William Saliba jan kati
An kori ɗan wasan na tawagar Faransa tun kafin a je hutun rabin lokaci.
Sai a wajen minti na 70 ne ɗan wasan Bournemouth, Ryan Christie ya jefa ƙwallo ta farko a ragar Arsenal bayan da aka ɗauko kwana.
Saura minti tara a tashi wasan ne kuma Kluivert ya ƙara ta biyu a bugun fenareti bayan golan Arsenal, David Raya ya yi wa Evanilson ƙeta a yadi na 18.
Da wannan sakamako Arsenal ta yi rashin nasararta ta farko a kakar wasa ta bana, yayin da ita kuma Bournemouth ta kawo ƙarshen rashin nasara huɗu da ta yi a jere, inda ta koma matsayi na 10 a kan teburi da maki 11.
Wannan sakamako babban koma baya ne ga Arsenal wadda ta rasa damar ɗarewa kan tebur kafin Liverpool ta karɓi bauƙuncin Chelase a gobe Lahadi.