Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bove ya farfaɗo daga suma bayan faduwa a fili ana tsaka da wasa
Ɗan wasan Fiorentina, Edoardo Bove ya farfaɗo daga suma, bayan da aka garzaya da shi asibiti, sakamakon faduwa kasa da ya yi a wasan Serie A da Inter Milan.
An tsayar da karawar a minti na 16 a lokacin da lamarin ya faru, likitoci sun duba lafiyarsa, sai aka tashi daga wasan bayan da aka ta fi da shi asibiti.
Fiorentina ta sanar da cewar ɗan wasan ya farfado a asibiti, harma ya yi magana da iyalansa da ƴan wasan Fiorentina, waɗanda suka garzaya domin duba lafiyarsa.
Za a ci gaba da auna koshin lafiyarsa, saboda a gano dalilin da ɗan wasan ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da taka leda a babbar gasar tamaula ta Italiya.
Bove na faduwa a cikin fili ne ya sa aka tsayar da karawar, inda ƴan wasa suka yi alamar likitoci su kai agajin gaggawa, waɗanda suka zagaye masu kula da shi a lokacin.
Daga nan aka ɗauke shi a kan gadon marasa lafiya zuwa motar da ta garzaya da shi asibiti, daga nan alkalin wasa ya bukaci da kowa ya bar filin.
Bove mai buga karawa daga tsakiya ya koma Fiorentina buga wasannin aro daga Roma a cikin watan Agusta da cewar za a ɗauke shi idan ya taka rawar gani.
Ya fara ci wa Fiorentina ƙwallo a cikin watan Oktoba da ya fuskanci Roma.
Ɗan wasan tawagar Italiya, ya taka mata leda tun daga matasa har zuwa ƴan kasa a shekara 21, amma ba a gayyace shi babbar tawagar ba kawo yanzu.