Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An sanar da ranar zaben shugaban kasar Senegal
Gwamnatin Senegal ta sanar da cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 24 ga watan nan na Maris.
Kasar dai ta rika fama da dambarwar siyasa tun da Shugaba Macky Sall ya dage zaben da ya kamata a yi a watan daya gabata na Fabarairu.
A wata sanarwa da majalisar ministocin ta fitar ta ce, ‘’Shugaban Jamhuriyar ya gaya wa majalisar ministoci cewa an tsayar da ranar Lahadi 24 ga watan Maris.
Kafin sanarwar ta ranar Laraba, hukumomi sun yi kokarin dage ainahin ranar zaben ta 25 ga watan Fabarairu zuwa watan Disamba, abin da ya haddasa mummunar tarzoma a kasar.
To amma daga baya kotun kolin kasar ta zartar da cewa dole ne a gudanar da zaben kafin ranar 2 ga watan Afirilu.
Tun da farko a ranar Larabar da yamma Mista Sall ya rushe gwamnati ya kuma maye gurbin Firaminista Amadou Ba da ministan cvikin gida Sidiki Kaba.
Ya yi hakan ne domin Mista Ba, wanda shi ne dantakarar hadakar jam’iyya mai mulki, ya samu damar mayar da hankalinsa kan yakin neman zabe in ji fadar shugaban kasar.
Shugaban wanda wa’adin mulkinsa zai kare a ranar 2 ga watan Afirilu ya kafe cewa bai taba niyyar neman tsayawa takara karo na uku ba.
Shugaba Sall ya yi wa’adinsa biyu kuma lokacin da aka zabe shi karon farko a 2012 ya yi alkawarin ba za iyi tazarce ba.
Sai dai duk da sauyin da aka samu game da ranar zaben, kawo yanzu babu wani sauyi a jerin sunayen ‘yantakara da za su fafata da juna , kuma abin nufi a nan shi ne jagoran 'yan hammaya da ke daure, Usman Sonko ba zai iya tsayawa takarar shugaban kasa ba.
Masu hamayya da shi na zarginsa da neman yi wa kundin tsarin mulki kasar juyin mulki.
Da dadewa ana kallon Senegal a matsayin kasar da mulkin dumukuradiyyarta ya samu gindin zama a nahiyar Afirka.
Ita ce kasa daya kawai da ke cikin dunkulen yankin Afirka ta Yamma da ba a taba yin juyin mulkin soja ba.