Rayuwa da tarihin matar da ta kirkiro batun tsarin iyali mai cike da ce-ce-ku-ce

Margaret Sanger in her younger days looking to

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

"A matsayin ku na iyaye mata Shin kuna da muradin samun babban iyali? Shin kuna son ƙara haihuwar yara? In ba kwa so, me ya sa kuka haife su? Kada ku kashe rai, amma ku yi ƙokarin ceto shi. Za a samu ingantattun bayanai daga wurin ungozoma.

Wannan na kunshe ne a cikin wani talla da ya bayyana a birnin New York a shekarar 1916 a kan batun asibitin tsarin iyali na farko a Amurka wanda Margaret Sanger ta kirƙiro.

A lokacin an haramta shan kwayoyin zub da ciki wanda kuma ya zamo abin ce-ce-ku-ce.

Ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba, aka rufe asibitin tare da tura Sanger zuwa gidan yari.

Sai dai bayan rasuwarta da cshekaru 50, abin da ta kirkiro ya zama sauyin rayuwa ga tsarin iyali a faɗin duniya.

Kafofin ƴaɗa labaru sun jinjina mata a matsayin matar da ta "ƙirkiro da tsarin iyali" da kuma samar da kwayoyin hana ɗaukar ciki.

A woman holding early birth control pills

Asalin hoton, Getty Images

Shahararriya mai ce-ce-ku-ce

Sai dai, dabarunta da kuma abin da ya sa ta fito da su, na cike da ce-ce-ku-ce. Haɗakarta da 'yan gwagwarmayar eugenics ya janyo zargi a kanta na nuna wariyar launin fata.

''Tarihin Sanger na cike da ce-ce-ku-ce,'' a cewar Sajam Ahluwalia, Farfesan tarihi da kuma ilimin mata a Jami'ar Arewacin Arizona, wacce kuma ta wallafa takarda kan batun tsarin iyal a India a shekarar 1877-1947.

''Bana tsammanin cewa abin ya ta'allaka ne kawai kan mata...sai dai ina tunanin cewa takaita mutane Sanger abun sauki ne...ya kamata mutane su san tarihinta,'' in ji Sajam yayin tattaunawa da BBC.

A woman fastens a mask to Margaret Sanger's face in Boston on 17 April 1929

Asalin hoton, Getty Images

Tasowa a cikin talauci

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An haifi Sanger a shekarar 1879 a jihar New York, ta kuma kasance ta sha ɗaya a cikin yaran mahaifinta.

Mahaifinta mai suna Michael, haifaffen ɗan Ireland ne mai sana'ar fasa duwatsu.

Sun kasance talakawa kuma suna rayuwa a cikin wani ɗan karamin gida da aka ƙera da itatuwa da kuma ƙarafa.

Mahaifiyar Sanger ta samu ciki sau 18, inda ta ɓarar da bakwai daga ciki.

Sanger ta fara ne a matsayin ungozoma mai taimakawa mutanen da ke fama da lalurori da suka yi tsanani, inda ta haɗu da wata mata da ta mutu kan lalurar ciki da kuma masu zubar da ciki a bayan titi.

"A lokacin akwai dokoki da suka hana aike da bayanai ta akwatin gidan waya kan batun tsarin iyali.

Akwai kuma wasu dokokin da suka haramta amfani da kwayoyin hana ɗaukar ciki a jihohi da dama,'' a cewar Elaine Tyler May, farfesa kan Tarihi da Ilimin Amurka a Jami'ar Minnesota, wacce kuma ta wallafa takarda mai suna America and the Pill.

Sanger ta jure abubuwa daga Cocin Katolika, da yake kallon shan kwayoyin hana ɗaukar ciki a matsayin laifi.

Hakkin yin tsarin iyali

A watan Maris din 1914, Sanger ta wallafa takarda mai suna Woman Rebel, wanda ya yi magana kan hakkin mata na yin koyi da tsarin iyali.

Ba a daɗe ba, hukumomi suka haramta amfani da takardar.

Daga baya Sanger ta tsere zuwa Ingila saboda tsoron kar a tura ta zuwa gidan yari.

A can, ta samu kwarin gwiwa da irin ayyukan Thomas Robert Malthus, wanda ya kalubalanci cewa mutane a duniya ba za su iya riko da ƙaruwar al'umma ba.

Ya bayar da shawarar daukar matakin kariya na kai da jinkirta yin aure.

Sai dai 'yan gwagwarmaya da ake kira neo-Malthusians, na matsawa na amfani da kwayoyi.

"Ta kuma fara duba wata hanya...tare da cewa tsarin iyali shi ne hanyar zaman lafiya da kuma kaucewa matsalar ƙarancin abinci,'' a cewar Dr Caroline Rusterholz, masaniya kan tarihi a Jami'ar Cambridge da ke Birtaniya, wacce kuma ke mayar da hankali kan al'umma da magunguna da kuma jinsi.

A birth control clinic opened secretly on First Avenue in New York City before World War One

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sanger ta kirkiro da asibitin tsarin iyali ne a lokacin da haramcin zubar da ciki ke aiki a Amurka

Asibiti na farko

Bayan komawar Sanger Amurka daga gudun hijira da take yi, sai ta buɗe asibitin tsarin iyali na farko a ƙasar a birnin New York da ya kasance gida ga talakawa da dama da kuma mata masu gudun hijira.

An kai samame asibitin kwanaki kalilan da fara aiki, inda aka kama Sanger.

Women and men with prams in front of the clinic

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata zaune da kekunan ɗaukar jarirai a gaban asibitin Sanger da ke titin Amber Brooklyn a New York, a watan Oktoban 1916

Duk da haka bata karaya ba, inda ta sake buɗe asibitin kwanaki kaɗan bayan faruwar lamarin, aka kuma sake kamata tare da zarginta da janyo damuwa cikin al'umma.

Bayan bayyana a gaban kotu a 1917, an sameta da laifi, inda aka yanke mata hukuncin zaman gidan yari na kwana 30 ko zaɓin biyan tara.

Amma ta zaɓi zaman gidan yari, inda ta rika bai wa fursunoni bayanai kan tsarin iyali.

"A lokacin da lamarin ya faru, ta zama shahararriya a Amurka. 'Yar uwarta ma na cikin gidna yari a lokacin, inda ta shiga yajin aikin cin abinci,'' a cewar wata da ta rubuta tarihin Sanger, Ellen Chesler.

Bayan sako ta, Sanger ta kalubalanci hukuncin da aka yanke mata, sai dai kotu ta yanke cewa likitoci za su iya bai wa mutane shawara kan magungunan tsarin iyali saboda dalilai na lafiya.

A crowd of people surrounding Sanger and her sister, Ethel Byrne, as they leave court

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan, wasu mutane ne ke kallo lokacin da Margaret Sanger da 'yar uwarta Ethel Byrne, ke barin harabar Kotu

Bala'i

A lokacin da take fama da shari'a a gaban kotu, ta kuma fuskanci bala'o'i daban-daban a rayuwarta.

A shekarar 1914, ta rabu da mijinta mai suna William, sannan a 1915, 'yarta ɗaya tilo Peggy, ta mutu lokacin da take shekara biyar.

Ta yi soyayya da maza da dama, har da wanda ke bincike kan dabi'un jima'i, Havelock Ellis da H G Wells.

A shekarar 1922, ta auri wani mai harkar mai James Noah H Slee.

Ya zama ɗaya daga cikin mutanen da suka marawa gwagwarmayarta baya.

'Yan gwagwarmayar Eugenics

Sanger ta nemi taimako daga 'yan gwagwarmaya da dama da kuma shiga haɗaka da kungiyoyin da ake gani da wuya a amince da manufofinsu.

"Ta haɗa kai da yan gwagwarmayar Eugenics... inda ta samu taimakon kuɗi daga wajensu,'' a cewar Rusterholz.

Cibiyar bincike ta Amurka mai suna National Humane Genome, ta ce za a iya inganta al'umma ne idan aka mayar da hankali kan takaita ƙaruwar al'umma''.

Sai dai ba a samu masu adawa da hakan ba a lokacin mulkin 'yan Nazi.

"Ta so ta ƴaki talauci ne, sai dai ta amince da wasu matakan 'yan gwagwarmayar Eugenics wadanda suka janyo matsala, kamar wadanda aka kawo kan masu buƙata ta musamman,'' in ji Rusterholz.

Margaret Sanger standing in front of a book shelf during her trial in Federal Court over her book The Woman Rebel

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sanger ta yi amfani da shawarwarin 'yan gwagwarmayar a takardar da ta wallafa na Woman and the New Race

Marubucin tarihi, Ellen Chesler, ya ce Sanger itama da matsalarta.

"Wasu 'yan eugenicist sun yi adawa da batun tsarin iyali ga mata matsakaita. Sun mayar da hankali kan yaruka da dama. Ba haka take ba. Tana son dukkan mata su haifi yara kaɗan.''

'Matalautan da basu da ilimin tsarin iyali'  

Gaɓa-ɗayan shekarun 1920 da 1930, Margaret Sanger ta yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashen duniya da dama, inda take ƙarfafa batun tsarin iyali a China da Japan da Korea da kuma India.

A wata wasika da ta rubutawa 'yan gwagwarmayar Eugenics na birnin Landan wadanda suka tallafa wa ziyarar da ta yi zuwa India a shekarar 1935, ta ce "zimmarta ne na ganin ta sanar da waɗanda basu da ilimin tsarin iyali su sani.''

Sanger speaking at the fifth International Birth Control Conference held in Tokyo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sanger ta kai ziyara zuwa yankin Asia don tallata batun tsarin iyali

Ta tallata wani hoda da ake amfani da shi a India.

Sai dai mutane da yawa sun yi ƙorafi kan hodan kan cewa yana kona fuska sannan akwai wahalar amfani da shi matuka ba idan ba a haɗa da magani ba.

"Hodar tana da karfi a kan tsarin iyali da kuma samun magungunan hana ɗaukar ciki, musamman ga marasa karfi. Sai dai fasahar bata aiki,'' a cewar Sanjam Ahluwalia.

Ta kuma haɗu da masu faɗa aji 'yan India da dama, kamar Mahatma Gandhi da Nobel laureate Rabindranath Tagore.

Yayin da Tagore ta marawa tsarin iyali baya, shi kuma Gandhi goyi bayan kariya na kai.

Sanger ta yi iyaƙar ƙokarinta, amma bata iya canzawa Gandhi ra'ayi ba.

Ƴaƙin duniya na biyu ya tilasta gwagwarmayar tsarin iyali a dukkan bangarori na yankin Atlanta.

Bayan nan, fargabar ƙaruwar al'umma ta bai wa masu ra'ayin na tsarin iyali damar samun kwarin gwiwa.

A wancan lokacin, Sanger da ta kasance cikin fushi kan magunguna da ake da su waɗanda kuma basa aiki, daga nan ta fara hankoron ganin an samu wasu hanyoyi masu sauki.

Ta rubuta mafarki da take na ganin ta wallafa wani takarda mai suna ''Magic Pill'' a shekarar 1939.

Mace 'yar gwagwarmaya ta farko da ta fara haɗaka da Sanger, ita ce Katharine McCormick, wata hamshaƙiya da mijinta ya rasu.

Ta kuma kasance wadda ta tallafawa binciken. Ta kuma ja ra'ayin masana da dama irinsu Dr Gregory Pincus domin shiga binciken.

Katharine McCormick wearing a sash showing the word 'Women' with a banner being held in the background

Asalin hoton, Getty Images

McCormick initially ta samar da $40,000. Daga bisani kuɗin sun ƙaru zuwa sama da $1m.

Bayan shekara goma, an gama haɗa maganin, amma akwai matsalar gwaji da kuma tabbatar da ingancinsa.

A lokacin an haramta zubar da ciki a Amurka. Amma a shekarun 1950, tawagar su Sagner ta kai ziyara zuwa Puerto Rico da Haiti.

An yi gwaji kan matan da ke gudun hijira da kuma waɗanda ke gida, duk da cewa da yawa basu san me suke sha ba.

"Hakane, an samu batutuwan cin zarafi. Babu ayar tambaya kan hakan,'' a cewar Elaine Tyler.

A shekarar 1965, Amurka ta yawaita maganin ga mata masu aure, sannan daga baya ga ɗaukacin mata a 1972.

Ƙasashe da dama sun amince su fara amfani da maganin su ma.

Sanger ta cika da farin ciki na ganin maganin ya samu karɓuwa kafin mutuwarta a shekarar 1966.

An dai sha zargin Margaret Sanger da batun nuna wariyar launin fata na shekaru da dama kan haɗakarta da 'yan gwagwarmayar eugenics da kuma ayyuka da ta yi da 'yan asalin Afirka mazauna Amurka.

Margaret Sanger, US activist for birth control

Asalin hoton, Getty Images

Al'ummomi bakaken fata sun gayyaceta domin ta kafa musu asibitoci.

Shirin ta mai suna ''Negro Project'' na da zimmar bayar da shawarwari kan kwayar maganin ne ga al'ummomi baƙaken fata a kudancin Amurka.

Sai dai hakan ya zamo abin ce-ce-ku-ce da baƙaken fata 'yan ƙasar suka soma, da kuma shan suka daga masu adawa da zubar da ciki.

A lokaci guda, ta jagoranci fara shirin bayar da ilimi kan lafiyar jima'i da zub da ciki da kuma kula da iyali.

Maganin ya zamo a matsayin ɗaya daga cikin magungunan tsarin iyali da aka fi amfani da shi a duniya baya ga kwaroron-roba.

A yanzu mata sama da miliyan 150 ne ke amfani da shi.