Zan iya farfaɗo da Mancester United- Ten Hag

Ten Hag

Asalin hoton, PA Media

An wallafa

Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce ƙungiyar na cikin wani irin yanayi amma har yanzu yana ganin shi ne mutumin da ya dace ya dakatar da koma baya a Old Trafford.

Nasarar da Newcastle ta samu da ci 3-0 a gasar cin kofin EFL ita ce babbar nasarar da suka samu a gidan Manchester United cikin shekaru 93.

Wannan shi ne rashin nasara na takwas da United ta yi cikin wasanni 15 da ta buga, mafi muni a farkon kakar wasa tun 1962-63.

Bayan da United ta sha kashi a hannun Manchester City a ranar Lahadi, shi ne karo na farko da United ta yi rashin nasara a wasannin gida da ci uku ko fiye da haka tun watan Oktoban 1962.

Ta yi rashin nasara a wasanni biyar cikin 10 na farko a gida a karon farko tun 1930-31.

Rashin ƙoƙarin 'yan wasan ya janyo magoya bayan ƙungiyar suka yi ma su ihu lokacin hutun rabin lokaci da kuma da aka tashi wasan, kuma hakan ya kawo ƙarin hasashe game da ko Ten Hag shine mutumin da ya dace da aikin.

"Na fahimci cewa wannan sakamakon bai yi masu daɗi ba kuma dole ne su yi korafi," in ji shi.

"Amma ina da yaƙinin cewa zan iya, a halin yanzu muna cikin wani mummunan kuma alhakin haka ya rataya a wuya na''. In ji Ten Hag.

United za ta kara da Fulham a wasanta na gaba a gasar Premier a ranar Asabar mai zuwa.