Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda majalisar dokokin Zamfara ta dakatar da ƴaƴanta tsawon shekara guda
Ana ci gaba da kiki-kaka game da batun mayar da wasu ƴan majalisar dokokin jihar Zamfara kan kujerunsu, bayan da majalisar ta dakatar da su kusan shekara guda da ta gabata.
Yanzu haka wasu daga cikinsu ma sun fara tunanin sauka daga kujerun na su, don a sake gudanar da zaben cike gurbi a mazaɓunsu ta yadda jama'arsu za su samu wakilci tun da duk wani kokari na ganin an warware matsalar bai kai ga gaci ba.
BBC Hausa ta ruwaito cewa a ranar 27 ga watan Fabrairu ne majalisar dokokin jihar ta Zamfara ta dakatar da wadannan yan majalisa 8 bisa zarginsu da gudanar da zaman majalisar ba bisa ka'ida ba.
Ƴan majalisar takwas su ne Bashir Aliyu (PDP-Gummi 1) Amiru Keta (PDP-Tsafe Ta Yamma) Nasiru Abdullahi (PDP-Maru Ta Kudu) Bashir Masama (PDP-Bukkuyum Ta Arewa) Faruku Dosara (APC-Maradun 1) Ibrahim Tukur (Mazabar APC-Bakura) Shamsudeen Hassan (APC Talata-Mafara Ta Arewa) da kuma Bashiru Sarkin-Zango (PDP-Bungudu Ta Yamma).
Ɗaya daga cikinsu Honarabul Ibrahim Tudu Tukur, ya faɗawa BBC Hausa cewa ''Matsalolin tsaro ne da suka ta'azzara ne suka sa muka je muka buɗe majalisa muka zauna muka yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da su dauki matakin gaggawa don magance wannan matsala, wannan shine abun da ya ɓata masu rai''
Ya ƙara da cewa majalisar malamai da majalisar masarautu da shi kansa shugaban PDP na jihar da wasu jagorori kamar tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari sun yi kokarin sasanta lamarin, amma dukka basu yi nasara ba.
To sai dai a nasa martanin mai magana da yawun majalisar dokokin jihar ta Zamfara Hamisu Alhaji Faro, ya ce suma suna na su kokarin domin ganin an sasanta wannan al'amari, amma abun da ke kawo cikas shine su ƴan majalisar da aka dakatar sun ki amincewa abun da suka yi kuskure ne ballantana su ba da hakuri a yafe masu.
''Sun karya dokoki na kundin tsarin mulki, suma sun san haka, kuma an gaya masu muna so a yafewa juna, amma su zo su ba wa shugabanni hakuri musamman shi kakakin majalisa, amma suka ce Wallahi tallahi baza su yi hakan ba''
Wasu daga cikin yan majalisar da aka dakatar dai na zargin gwamnan jihar Dauda Lawal da hannu a dakatar da su kasancewarsu yan jam'iyyar APC ne, sai dai kuma a cikinsu akwai hatta ƴan jam'iyyar gwamnan ta PDP.
Wannan al'amari dai ya sa kananan hukumomin yan majalisar sun rasa wakilci a majalisar dokokin jihar tsawon shekara guda, wani abu da ya sa masu sharhi ke ganin zai haifarwa mazaɓun na su gagarumar asara, saboda rashin waklcin da zai rika kai kokensu gaba.