Ƴan Real Madrid da za su kara da Mallorca a La Liga

An wallafa

Real Madrid za ta buga wasan farko a 2024 a karawar La Liga mako na 19 da karbar bakuncin Real Mallorca a Santiago Bernabeu ranar Laraba.

Real Madrid mai maki 45 tana matakin farko a kan teburin La Liga da maki 45, iri daya da na Ginora ta biyu.

Ita kuwa Mallorca mai maki 18 tana ta 14 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Sipaniya, bayan wasa 18.

Real Madrid da Mallorca sun hadu a La Liga karo biyu a bara, inda kungiyar da ke Bernabeu ta ci 4-1 ranar 11 ga watan Satumbar 2022.

A wasa na biyu Mallorca ta yi nasarar cin 1-0 ranar 5 ga watan Fabrairun 2023.

Haka kuma a ranar ta Laraba, Girona, wadda take ta biyu a teburin za ta karbi bakuncin Atletico Maadrid, wadda take ta ukun teburi mai maki 38.

Wasannin La Liga da za a buga ranar Laraba:

  • Granada da Cadiz
  • Celta Vigo da Real Betis
  • Real Madrid da Real Mallorca
  • Girona da Atletico Madrid

Ƴan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Lunin, Kepa da kuma Fran.

Masu tsaron baya: Carvajal, Lucas V., Fran García, Rüdiger da kuma Carrillo.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Valverde, Tchouameni, Ceballos, Arda Güler da kuma Nico Paz.

Masu cin kwallaye: Vini Jr., Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.