Mason Mount zai yi jinyar 'yan makonni

An wallafa

Dan wasan Manchester United Mason Mount ba zai buga wasa biyu a Premier League, sakamakon jinya da zai yi.

Kungiyar ta ce tana sa ran Mount zai yi jinya har sai bayan hutun wasannin kasa da kasa saboda karamin rauni da ya samu a wasan da Tottenham ta doke United da ci 2-0 a karshen makon da ya gabata.

Mount ya koma United ne daga Chelsea a watan Yuni a kan fam miliyan 55.

Kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama za ta karbi bakuncin Nottingham Forest a ranar Asabar, sannan ta ziyarci Arsenal a ranar 3 ga Satumba.

Ana shakkun cewa dan wasan na Ingila mai shekara ba zai iya buga wasan neman cancantar shiga gasar Euro 2024 da Ingila za ta buga da Ukraine a ranar 9 ga Satumba.