Maguire ya ce rashin barin United ya sa yana komawa kan ganiya

Harry Maguire

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Harry Maguire ya ce yanzu yana ganin alfanun da bai bar Manchester United ba, domin bayyana kwazonsa cikin 'yan wasan Erik ten Hag 11 da ke buga wasa.

Maguire ya buga wasan Premier League na biyar a bana, yayin da United ta doke Luton Town 1-0 a Old Trafford ranar Asabar.

Ba wanda ya dauka dan kwallon Ingilan zai koma buga wa United wasannin sosai, bayan da ya koma zaman benci, ko sauyin dan kwallo daga baya.

To amma yanzu Maguire na buga kwallon da ya dace tun daga wasa da Brentford ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya mayar da Varane zaman benci har karo hudu.

Maguire ya gwammace ya ci gaba da taka leda a Old Trafford maimakon ya koma West Ham kan fara kakar bana, bayan da United ta amince da tayin da aka yi wa mai shekara 30.

''Wasan da na buga a bara ba su da yawa, ba na samun damar buga wasannin kamar yadda nake bukata,'' in ji mai tsaron bayan tawagar Ingila.

''Na samu damar da zan buga wasa biyu ko uku sai na kamu da rashin lafiya, sannan ga rauni da naji har karo biyu, hakan ya sa ban samu damar nuna kwazo na ba.''

Wasa takwas aka fara da Maguire a bara a Premier League, inda Ten Hag ya ce dan kwallon bai da gogewa wajen murza kwallo a bangarensa na hagu mai tsaron bayan yana da rauni a bangaren.aga nan

Daga nan ne ya koma zaman benci, inda ake amfani da Varane, maimakon Maguire, wanda ya sa kwazo ya kuma karbe gurbinsa.