Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool na zawarcin Camavinga, Manchester City ke harin Semenyo
Liverpool sun taya ɗan wasan Real Madird mai shekaru 23 Eduardo Camavinga, kan kudi fam miliyan 52.5 (Euro miliyan 60). (Caughtoffside)
Everton ta ce ba zata saurari wani tayi ba, kan ɗan wasanta mai shekaru 25 Iliman Ndiaye ba, domin ba ta da niyar shirin da shi ba ga Liverpool. (Teamtalk)
Manchester City na duba yiwuwar ɗauko ɗan wasan Bournemouth mai shekaru 25 Antoine Semenyo, kan fam miliyan 65, a watan Janeru mai zuwa. (Times - subscription required)
Jurgen Klopp zai ci gaba da zama a Red Bull, yayin da take ƙasa, take dabo na yiwuwar komawarsa Liverpool, inda har Arne Slot ya yanke barin Anfield. (Telegraph - subscription required)
Daraktan Wasannin Arsenal Andrea Beta na jagorantar aniyar ƙungiyar wajen gani ta ɗauko ɗan wasan Elche mai shekaru 20 Rodrigo Mendoza, gabanin kakar siyen ƴan wasa a watan Janeru.(Football Insider)
Chelsea da Tottenham sun shirya gogayya da Arsenal wajen ɗaukar Mendoza. (Teamtalk)
Manchester United ta ce da gaske ta ke a ƙoƙarinta na ɗauko ɗan wasan Real Madrid Federico Valverde, kuma za ta yi maraba da dukkan wani abu da ɗan wasan ya gabatar mata idan har yana son komawa ƙungiyar don taka leda a Old Trafford.(Fichajes - in Spanish)
Daraktan wasannin Barcelona Deco ya ce Marcus Rashford ɗan wasan Manchester United a ke taka leda a Barcelona a masatyin aro, na jin daɗin zamansa a ƙungiyar kuma suna son ya ci gaba da zama a ƙungiyar, idan da hali. (Times - subscription required)
Manchester United na dab da kamala tattaunawa wajen ɗauko ɗan wasan Fortaleza CEIF Cristian Orozco, nan da yan kwanaki, yayin da za a kamala cinikin nan da watan Yuli. (Daily Star)
Ƴan wasan Tottenham sun yi bayani dalla-dalla kan rashin jin daɗinsu kan yadda magoyabayan ƙungiyar, a yayin wata taron tattaunawa. (Telegraph - subscription required)