Chelsea ta nada Vivel sabon daraktan wasanninta

Vivel

Asalin hoton, OTHER

An wallafa

Chelsea ta nada Christopher Vivel, a matsayin sabon daraktar wasannin Kungiyar.

Vivel wanda dan kasar Jamus ne na da shekaru 36, kuma kafin sabon mukamin nasa shi ne ke jagorantar masu farautar yan wasa a RB Salzburg a Austria.

Shi ne ya yi uwa da makarbiya wurin kawo Erling Haaland Red Bull Salzburg a 2019.

Vivel zai maye gurbin tsohon golan Chelsea Petr Cech, wanda ya bar kungiyar bayan shekaru uku.

Mai kungiyar Todd Boehly ya ce matashin zai taimaka wa koci Graham Potter.

''Ayyukan da ya yi a Jamus da Austria an gani a kasa. Kuma muna da kwarin gwuiwa cewa zai cigaba irin wadannan ayyuka a Chelsea.'' In ji Boehly.

A nasa jawabin Vivel ya ce '' Chelsea ta dauko wani jan aiki na habaka kwallon kafa, kuma ina alfahari da zuwa kungiyar.''

Chelsea za ta dawo buga wasannin Premier League a ranar 27 ga watan Disamba bayan dawowa hutun gasar kofin duniya, inda za ta kara da Bournemouth a filinta na Stamford Bridge da ke London.