Nunez ba zai yi wa Liverpool wasan Premier uku nan gaba ba

Asalin hoton, Getty Images
Sabon dan kwallon da Liverpool ta dauka a bana Darwin Nunez, ba zai buga wa kungiyar wasa uku a gasar Premier League ba.
Hakan ya biyo bayan jan katin da aka yi masa a wasan farko da ya fara yi a Anfield ranar Litinin da Crystal Palace da suka tashi 1-1.
An bai wa Nunez jan kati, bayan da suka koma zagaye na biyu a lokacin Palace ta ci kwallo daya.
Dan kwallon tawagar Uruguayan ya yi wa mai tsaron bayan Palace, Joachim Andersen gware da ka a wasa na biyu da Liverpool ta raba maki.
A makon farko Liverpool ta tashi 2-2 a gidan Fulham, inda Nunez da Mohamed Salah ne suka ci kwallayen.
Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp na fama da karancin masu cin kwallaye, bayan da Diogo Jota ke jinya, Roberto Firmino bai buga fafatawa da Palace ba.
Nunez wanda ya ci wa Liverpool kwallo daya a wasan Premier League ta bana, ba zai buga haduwa da Manchester United ba ranar Litinin a Old Trafford.
Kawo yanzu ba a da tabbaci ko Firmino zai warke kafin litinin domin ya buga wa Liverpool wasan mako na uku a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Wasa na gaba da dan kwallon mai shekara 23 da ba zai buga ba shi ne da Bournemouth a Anfield ranar Asabar 27 da wanda Liverpool za ta kece raini da Newcastle United.
Yin keta da ganganci kan sa a kara hukuncin zuwa wasa hudu, amma ana sa ran dan kwallon wasa uku ne ba zai buga ba.











