Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba zan daina wasa da kwallo ba, da shi aka sanni in ji Antony
Dan wasan Manchester United na gaba Antony ya ce, "ba zai daina abin da ya fito da ni ba aka san ni" bayan wani wasa da ya yi da kwallo a Europa wanda ya janyo masa suka.
Antony ya yi zagaye biyu da kwallo a tsakanin kafafunsa a ranar Alhamis a wasan da Manchester ta yi nasara a kasan Sheriff Tiraspol da ci 3-0.
Erik ten Hag bayan an kammala wasan ya ce "za mu gyara masa" idan ya yi wasa da kwallo mara dalili a cikin wasa.
"An samunmu kan abin da muka kware a kai, ban zan daina yin abin da ya kawo ni nan ba," kamar yadda Antony ya rubuta a safinsa na Instagram.
A ranar Juma'a dan wasan mai shekara 22 ya wallafa wannan sako.
Bayan da Antony ya yi wasan, sai ya buga kwallo wajen ragar Sheriff.
Ten Hag ya musanta cewa wannan ne dalilin da ya sanya ya cire dan wasan da aka saya £85m a hutun rabin lokaci.
"Ni ba ni da matsala da wasa da kwallo matukar zai yi amfani," in ji kocin dan kasar Netherland wanda ya yi aiki da Antony a Ajax.
"Ina bukatar ya kara kokari - ya kara karfafa kansa, ya kara ci gaba da kai hare-hare da kuma yawan cin kwallo.
"Lokacin da zai yi irin wannan matukar zai yi amfani. Idan ba za a kwace kwallon ba, to ai babu damuwa - amma idan wasa ne da nufin wasa, to ai dole mu yi masa gyara."