Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rashford ya ci kwallo na 100 a Man United a wasan West Ham
Manchester United ta yi nasara a kan West Ham da ci 1-0 a wasan mako na 14 a gasar Premier League ranar Lahadi a Old Trafford.
Marcus Rashford ne ya ci kwallon a minti na 38 kuma na 100, ya zama na 22 da ya ci wa Manchester United kwallo 100.
Na karshe mai wannan bajintar a United shi ne Wayne Rooney, tun bayan 2009.
United ta koma ta biyar da maki 23 a kan teburin Premier League, ta yi kasa da Chelsea zuwa mataki na shida mai maki 21.
United za ta buga Europa League karawar cikin rukuni na karshe da Real Sociedad da za suyi a Sifaniya.
Wasan da suka kara a tsakaninsu a bara:
2021/2022
Premier League Asabar 22 ga watan Janairun 2022
- Man Utd 1 - 0 West Ham
League Cup Laraba 22 ga watan Satumba 2021
- Man Utd 0 - 1 West Ham
Premier League Lahadi 19 ga watan Satumba 2021
- West Ham 1 - 2 Man Utd
Wasu batuwan da ya kamata ku sani kafin karawar ta ranar Lahadi.
Manchester United ta yi nasara a kan West Ham a wasa hudu baya a Premier League.
West Ham ba ta ci wasa ba daga 14 baya da ta ziyarci Old Trafford, inda ta yi canjaras uku aka doke ta fafatawa 11 a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Manchester United
Manchester United ta yi rashin nasara a wasa daya daga 14 baya da ta buga a gida, wadda ta ci takwas da canjaras biyar.
United ta sha kashi a wasa 10 daga 31 da ta yi a shekarar 2022, mafi muni kenan a tarihin kungiyar tun bayan 12 da aka doke ta a 1990.
Marcus Rashford' ya ci West Ham kwallo uku a lik, kuma a lokacin da yake shiga wasan daga baya, har da wadda ya zura a raga a minti na 90 a bara.
Cristiano Ronaldo ya zura kwallo shida a wasa tara a Premier League da ya fuskanci West Ham.
West Ham United
West Ham ta yi rashin nasara a wasa 10 baya daga 14 da ta yi a waje da cin biyu da canjaras biyu.
Wasa biyu ne kwallo bai shiga ragar West Ham daga 17 da ta buga a lik a waje ba.
Kwallo uku kacal West Ham ta zura a raga a wasannin waje a lik, masu karancin zura kwallaye a raga a waje a bana, sun hada da Nottinghma Forest da Wolves.
Cikin wasa 15 da David Moyes ya ziyarci Old Trafford a matsayin koci bai ci karawa ko daya ba, wanda ya yi canjaras hudu aka doke shi fafatawa 11.