Dan wasan Man United Telles na daf da komawa Sevilla

An wallafa

Dan wasan Manchester United dan kasar Brazil, mai tsaron baya, Alex Telles na daf da komawa buga wasannin aro a Sevilla zuwa karshen kakar nan.

Telles bai da makoma a Old Trafford karkashin sabon koci Erik ten Hag a bana, wanda ya dauko Tyrell Malacia, saboda haka dole a bayar da aronsa ko yayi zaman benci.

Bayan da Luke Shaw ke tsare bayan United daga hagu, an yi amfani da Telles a wasannin sada zumunta a gurbin mai tsaron baya daga tsakiya.

To sai dai ba zai samu buga gurbin daga tsakita ba a Premier League ta kakar nan, bayan da United ta dauko Lisandro Martinez daga Ajax.

Zaman Telles a benci zai sa Brazil kenan ta kasa kirsansa buga mata gasar kofin duniya a Qatar a bana, saboda haka buga La Liga zai kara fito da kwazonsa.

Tawagar Brazil ta gayyaci dan kwallon mai shekara 29 a watan Janairu, bayan wata 14 rabon da ta bukace shi ya yi mata tamaula.

Telles ya koma United a 2020 daga FC Porto kan fam miliyan 13.6.