Fatan Messi na lashe kofin duniya na nan daram

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Fatan da Lionel Messi ke yi na lashe gasar cin kofin duniya na nan lafiya kalau bayan da kungiyarsa ta Argentina ta doke Netherlands bayan sun shafe minti 120 babu wanda yayi galaba, har sai da suka buga fenareti a filin wasa na Lusail da ke Qatar.

Tun a cikin minti na 35 Messi ya taimaka wa Nahuel Molina da kwallon da ta ba Argentina damar shan gaban Netherlands, sannan a minti na 73 ya zura ta biyu bayan da aka ba kasarsa fenariti bayan da Denzel Dumfries ya janyo wa kasarsa koma baya da ya afka wa Marcos Acuna.

Sai dai kocin Netherlands Louis van Gaal ya shigar da dan wasa Wout Weghorst, wanda ya zura kwallaye biyu ana daf da kammala wasan.

Wannan ya sa aka yi karin lokaci amma babau kasar da ta sami galaba kan abokiyar karawarta, kuma daga nan aka buga fenareti.

Golan Argentina Emi Martinez ya sami damar hana kwallaye biyu shiga ragarsa, daga kwallayen da Virgil van Dijk da Steven Berghuis na Netherlands suka buga a bugun na daga kai sai mai tsaron gida.

Messi ya zura tasa kwallon, wanda ya taimaka wajen ba kasarsa nasara kan Netherlands.

A karshe Argentina ta lashe wasan da ci 4-3.