Netflix zai biya ma'aikacin jirgin da zai dauka haya dala 385,000 a shekara

Netflix

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Netflix na shirin ɗaukar ma'aikacin jirgi haya, da zai yi aiki a ɗaya daga cikin jiragen da kamfanin yake da su, tare da biyansa dala 385,000 a shekara.

Kamfanin wanda ke haska fina-finai ya ce yana buƙatar ma'aikacin da yake da ƙwarewa ta fuskar kula da tsaftar cikin jirgi da hidima ga kwastomomi.

"A shekarar da ta gabata ne kamfanin na Netflix ya rage ɗaruruwan ayyukansa, bayan da ya fuskanci raguwar abokan huldarsa.

Kamfanin ya ce yana ƙayyade albashin ma'aikatansa ne ta hanyar la'akari da ƙwarewa da gogewar aiki da suke da ita.

Ainihin wajen aikin shi ne California, to amma aikin zai buƙaci tafiye-tafiye zuwa ciki da wajen Amurka.

''Sashen sufurin jiragen sama na Netflix zai samar da ingantacciyar zirga-zirga cikin tsaro da sirri'', in ji kamfanin.

Kamfanin ya ƙara da cewa ma'aikacin zai taimaka wa Netflix wajen gunadar da ayyukansa a faɗin duniya ta yadda zai ci gaba samar da farin ciki a ga kwastomominsa a faɗin duniya.

Daga cikin ayyukan da sabon ma'aikacin jirgin zai gudanar a cikin jirgin nasa mai suna ''Super Midsize Jet'' sun haɗar da duba kayayyakin saukar gaggawa na fasinjoji da na ma'aikatan jirgin kafin tashinsa.

Haka kuma dole su iya ɗaukar kayan da nauyinsa ya kai kiligiram 13.6kg a lokacin da ake yi wa jirgin lodin kaya.

Matsakaicin albashin ma'aikacin jirgi a Amurka ya haura dala 62,000 a shekara, kamar yadda hukumar ƙididdigar ma'aikata ta Amurta ta bayyana.

A lokacin da BBC ta tuntuɓi kamfanin na Netflix, mai magana da yawun kamfanin ya ce ba zai yi jawabi kan yadda kamfanin yake lissafa albashin ma'aikatan jirgi ba.

Ranar Alhamis ne kamfanin zai bayyana kuɗin da ya samu a cikin wata ukun ƙarshe na shekarar 2022.

A shekarar da ta gabata Netfilx ya ce ya samu ƙarin masu bibiyarsa har kusan miliyan 2.4 a cikin wata uku zuwa ƙarshen watan Satumba, lamarin da ya taimaka wajen farfaɗo da kamfanin.

A baran ne dai kamfanin ya rage ɗaruruwan ayyuka domin magance matsalar kuɗi da ta tattalin arziki.