Varane zai bar Man United a karshen kakar bana

An wallafa

Mai tsaron bayan Manchester United, Raphael Varane zai bar Old Trafford a karshen kakar nan, wanda kwantiraginsa zai kare a lokacin.

Mai shekara 31 ɗan kasar Faransa, ya koma United da taka leda a Yulin 2021 daga Real Madrid kan £34m, wanda ya buga wasa 93 a kungiyar Premier League.

Tsohon ɗan wasan tawagar Faransa ya bayar da gudunmuwar da United ta lashe Carabao Cup a 2023 a kakar da Erik ten Hag ya karbi aiki, wanda ya ci Newcastle United a wasan karshe.

Varane ya dauki kofin La Liga uku da Champions League hudu a lokacin da ya taka leda a Real Madrid, daga nan ya koma Old Trafford karkashin Ole Gunnar Solskjaer.

Ɗan kwallon ya lashe kofin duniya tare da Faransa a 2018 daga baya ya yi ritaya daga buga wa kasar tamaula a cikin Fabrairun 2023.

Mai tsaron bayan na jinya tun ranar da Chelsea ta ci United 4-3 ranar 4 ga watan Afirilu, kuma saura wasa uku ya rage a gaban United a bana.

United za ta kara da Newcastle United ranar Laraba daga nan ta kara a wasan karshe a Premier League da Brighton ranar Lahadi 19 ga watan Mayu.

Kungiyar da Ten Hag ke jan ragama tana ta takwas a teburin Premier League za ta fuskanci Manchester City a FA Cup wasan karshe a Wembley ranar Asabar 25 ga watan Mayu.