Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Watakila Ronaldo ya ci gaba da taka leda a Man United
Cristiano Ronaldo ya buga wa Manchester United wasan sada zumunta da Rayo Vallecano ranar Lahadi a Old Trafford.
Kungiyoyin biyu sun tashi 1-1 a wasan sada zumunta don tunkarar kakar da za a fara cikin watan Agusta, wasan farko da Erik ten Hag ya ja ragama a gida.
'United ce ta fara cin kwallo ta hannun Amad Diallo daga baya Rayo ta farko ta hannun Alvaro Garcia.
Tun da aka kammala kakar da ta wuce ake ta rade-radi kan makomar Ronaldo a Old Trafford.
Mai shekara 37 na son barin United a bana, domin ya samu damar buga Champions League a wata kungiyar.
United ta karkare a mataki na shida a kakar da ta wuce, dalilin da ya sa za ta buga Europa League kenan a bana, gasar da kyaftin din Portugal bai yi shirin yi ba.
Dan kwallon bai bi United wasannin sada zumunta da ta yi a Thailand da kuma Australia, saboda da wani dalili na radin kansa.
Filin wasa na Old Trafford ya rude da tafi a lokacin da Ronaldo ya ja ragamar 'yan kwallo shiga fili don motsa jiki, kafin fara wasan na sada zumunta.
Hakan na nuna cewar magoya bayan United ba sa fushi da kyaftin din Portugal, suna kuma bukatarsa idan ya amince zai buga Europa, saura kaka daya yarjejeniyarsa ya kare a Old Trafford.
Wasu na ganin Ronaldo wanda manyan kungiyoyi suka ki karbarsa a tayin da aka yi musu, zai amince ya ci gaba da taka leda a United.
United za ta fara wasan farko a gasar Premier League ranar 7 ga watan Agusta da Brighton.
Suma sabbin 'yan wasan da United ta dauka a bana, Christian Eriksen da kuma Lisandro Martinez sun buga mata wasan na sada zumunta ranar Lahadi.