Al-Hilal ta gabatar da Neymar a gaban magoya bayanata

fg

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gabatar da Neymar a gaban magoya bayan Al-Hilal wanda aka saya a kuɗi mai yawa daga PSG
An wallafa

Al-Hilal ta gabatar da ɗan wasan gaban Brazil Neymar ga magoya bayanta bayan kammala ɗaukarsa da ta yi a matsayin sabon ɗan wasanta.

An ta harba wuta mai kyalkyali sama a filin wasa na King Fahad da ke Riyadh, lokacin da ɗan wasan mai shekara 31 ya bayyana sanye da shuɗiyar rigar ƙungiyar a karon farko.

Wani jirgi mara matuƙi ya watso wasu ledoji da suka rubuta sunan Neymar a filin wasan da ke ɗaukar sama da mutum dubu 68.

Neymar ya koma gasar Saudiyya daga PSG a ranar Talata kan kuɗi fan miliyan 77.6.

Zuwan ɗan wasan dai ya nuna yadda Saudi ke ci gaba da kashe kudi wajen ɗauko manyan 'yan wasan nahiyar Turai zuwa gasar ƙasar.

Karim Benzema da N'Golo Kante da Jordan Henderson da Ruben Neves da Sadio Mane da kuma Roberto Firmino dukan su suna Saudiyya, yayin da ɗan wasan Portugal Cristiano Ronaldo ya daɗe da koma wa Al-Nassr a farkon wannan shekarar daga Manchester United.

Ana sa ran Neymar zai fara bugawa Al-Hilal wasa a ranar Alhamis a wasan da za ta fafata da Al-Raed.

fg

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A hukumance Neymar ya zama sabon ɗan wasan Al-Hilal
fg

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubban magoya baya ne suka halarci gabatar da ɗan wasan
fg

Asalin hoton, Getty Images

fg

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rahotanni na cewa za a riƙa biyan Neymar fan miliyan 129.2 a duk shekara a Saudiyya
fg

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Komawar Neymar Saudiyya dai na nuna yadda ƙungiyoyin gasar ke ci gaba da kashe kuɗi wajen sayan 'yan wasan Nahiyar Turai