Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake samu karuwar wakokin kyamar Musulmai a India
Sandeep Chaturvedi, mai shekara 26, na shirin yin sabuwar wakarsa a wani dakin rera wakoki da ke birnin Ayadhya a Jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya.
Wakar da yake rerawa kan masallaci ne da ya zama abin ce-ce-ku-ce bayan mabiya addinin Hindu sun yi ikirarin cewa suke da hakkin bauta a yanki.
Wakar na dauke da baituka kan wariyar da ake nuna wa Musulmai. Amma Chaturvedi na cewa wakar za ta sake farfado da fannin nishadi.
Wakar Chaturvedi na cikin wakokin da ke tashe a Youtube da wasu shafukan sada zumunta inda masu tsattsauran ra'ayi na addinin Hindu ke yada kalaman batanci kan Musulunci.
Yayin da mutane ke iya cin karensu ba babbaka da kalaman kiyayya a India, baitin wakar na tattare da cin mutunci da barazana.
Suna yin kalaman kiyayya ne bisa tunanin cewa masu bin addinin Hindu sun sha bakar wahala a tsawon daruruwan shekaru a hannun Musulmi - don haka yanzu lokacin ramuwa ne.
Masu rubuce-rubuce da sharhi kan siyasa irin su Nilanjan Mukhopadhyay sun ce baya ga batun samar da kudaden shiga, irin wadannan wakoki na jan hankali kan mawaka.
Amma a wurinsa, wannan ba waka ba ce. "Wannan kira ne na yaƙi. Kamar ana son amfani da waka ne domin nasarar yaƙi.
Wannan rashin sanin dacewa ne a fannin waka kuma an kwashe shekaru da dama ana yin hakan."
Chaturvedi ya soma waka da wakokin bege shekaru 10 da suka gabata, amma ya sauya salo 'yan shekarun baya lokacin da ya yanke shawarar soma wakokin bautar "Hindu da na hadin-kan kasa".
A cewarsa ya soma wannan salon ne a wani kokari na sauya tunani. Ya yi fice lokacin da wata wakarsa ta yi tashe a 2016 tsakanin 'yan Hindu.
Amma salon wakar kai-tsaye yake fitar da sakonta: gargadi kan al'ummar Musulmai game abin da zai faru ranar da 'yan Hindu suka yunkuro.
Chaturvedi ya ce miliyoyin mutane sun kalli wakar a shafin Youtube kafin a dakatar da shafinsa bayan dubban korafe-korafe.
Ya yi zargin cewa Musulmai na kai korafi kan wakarsa saboda rashin dacewa.
Ya fuskanci barazanar rasa miliyoyin mabiya amma ya ki hakura da kudin da yake samu a Youtube.
Ya ce yana kashe dala 253 wajen nadar bidiyon waka. "Ba wai wani kudin kirki nake samu a Youtube ba. Abu mafi muhimmanci shi ne ficen da na yi a matsayin mawakin juyin-juya-hali," a cewarsa.
Tun bayan wannan lokaci Chaturvedi ya kirkira sabon shafinsa a Youtube.
Amma adadin masu kallon bidiyonsa bai taka kara ya karya ba.
Sai dai yana fatan sauya haka da sabuwar wakarsa. Duk da cewa ana zargin yana kai wa Musulmai hari ta wakokinsa, ya ƙi yarda ya nemi afuwa.
Upendra Rana shi ma wani mawaki ne da ke garin Dadri kusa da birnin Delhi.
Ya ce babban burinsa shi ne ya "gyara" tarihi kuma ana yin wakokinsa ne ga gwarazan mabiya addinin Hindu inda a wakokin ake nuna shugabannin Musulmai a matsayin mugaye.
Rana ya ce yana samun kudaden shiga sosai daga bidiyon da yake wallafawa a Youtube. "Muna kawo kudaden ketare a Indiya. Youtube na biyanmu da daloli," a cewarsa.
Tun lokacin da Rana ya sauya salon wakarsa daga na addini da soyayya zuwa tarihi, ya zama wani tauraro da ake ji da shi a Dadri.
Yana da kusan mabiya 400,000 a Youtube kuma da dama daga cikin wakokinsa miliyoyin mutane sun kalla.
Rana ya ce yana kashe dala 100 wajen nadar bidiyon waka.
Tana da tawaga ta musamman nake nada da tace bidiyonsa har matakin fitarwa.
Mista Mukhopadhyay ya ce amfani da waka a matsayin makamin yakar tsiraru abu ne da aka jima ana yi - tun lokacin kaka da kakanni.
Ya ba da misali da wani shirin Ayodhya na 1989 da masu ra'ayin rikau na Vishwa Hindu Parishad suka shirya, abin da ya tunzura mabiya addinin Hindu suka rusa masallacin Babri a 1992.
"Kafin wannan lokaci, an nadi maganarta tana ta yawo. Suna kunshe da wakoki addini da kalaman tunzuri da ke da alaka da Ram Janmabhoomi da Hindu ke bautawa"
Shekaru 30 bayan aukuwar hakan, sai na fahimci idan kana son zama a Indiya to ka iya bakinka, ka sa iyakarka kuma kar ka yi wa kowa kallon raini."
"Matasa na son wadannan wakoki saboda suna zaburar da su," a cewar Pinky Chaudhary, da ke wakiltar kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Hindu Raksha Dal.
Yana da ja kan yadda wadannan wakoki ke taimakawa wajen wayar da kawunan matasa.
"Ina jin wani karfi a jikina idan na saurari irin wadannan wakoki. Suna tunasar da ni irin abubuwan da muka fuskanta da kuma matsayin da muke," a Vijay Yadav.
Mr Yadav, mai shekara 23, fitacce ne a fannin zane-zane da ke karatu a Kwalajen Lalit Kala Akademi ta India, ya ce yana jin dadin sauraron irin wadannan wakoki.
A lokaci iri wannan, wakokin da ke kunshe da cin mutunci lokacin da Hindu da Musulmi ke hamayya da juna ana samun tashe-tashen hankula.
A wasu lokutan ma, rigimar da wadannan wakoki ke haifarwa irin nasu Chaturvedi a 2016 - na tunzura munanan rikici.
Chaturvedi ya musanta wadannan zarge-zarge. "Ni burina shi ne wayar da kawuna ta hanyar wakokina. Babu ribar da ake samu daga soyayya. Dole mu yi yaki domin kwace ain da yake namu."