Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Japan ta yaga baraka Jamus a Gasar Kofin Duniya a Qatar
Japan ta doke Jamus da ci 2-1 a wasan farko a rukuni na biyar a Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar da suka kara ranar Laraba.
Ilkay Gundogaan ne ya ci wa Jamus kwallon farko a minti na 33 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Kenan ya zura tara a wasa 22 da ya yi wa tawagar Jamus, tun bayan fara kakar 2021, bayan cin takwas daga karawa 42 tsakanin 2011 zuwa 2022.
Ritsu Doan shi ne ya farke kwallon da aka ci Japan, sannan Takuma Asano ya kara na biyu saura minti takwas lokaci ya cika.
Karon farko da Japan ta ci karawar da aka fara zura mata kwallo a raga a Gasar Kofin Duniya da canjaras biyu da rashin nasara bakwai kafin ranar Laraba.
Wannan shi ne karon farko da Jamus ta yi rashin nasara a karawar da ta fara cin kwallo kuma kan hutu tun bayan 1978 a hannun Australia da ci 3-2.
Jamus, wadda ta yi ta karshe a cikin rukuni a Rasha a 2018 ta barar da damarmaki da yawa tun kan hutu da bayan da suka koma zagaye na biyu.
Jamus za ta fuskanci kalubale a rukuni na biyar da za ta buga wasan gaba da Sifaniya ranar Lahadi, sannan ta buga da Costa Rica.
'Yan wasa takwas a tawagar Japan suna taka leda a Jamus, yayin da bakwai daga ciki ke buga gasar tamaula ta Japan.
Mai tsaron bayan, Yuto Nagatomo ya zama na farko da ya buga Gasar Kofin Duniya hudu, shi ne kan gaba a yawan buga babbar Gasar tamaula ta duniya mai 12.
Tuni ya sha gaban Makoto Hasebe da kuma Eiji Kawashima da kowanne ya buga wa Japan karawa 11.