An ci Arsenal a karon farko a Premier League a bana

An wallafa

Newcastle United ta yi nasara a kan Arsenal da ci 1-0 a wasan mako na 11 a gasar Premier League da suka buga ranar Asabar a St James Park.

Kungiyar da Eddie Howe ke jan ragama ta ci kwallon ta hannun Anthony Gordon tun sauran minti 26 a tashi daga fafatawar.

Tun bayan da Newcastle United ta yi rashin nasara a wasa uku an kasa doke ta a karawa bakwai a babbar gasar tamaula ta Ingila.

A bara da kungiyoyin suka hadu a Premier League, sun tashi ba ci a Emirates, sannan Gunners ta je ta doke Newcastle 2-0.

Tun kan karawar ta ranar Asabar, Arsenal ta ci Newcastle karo 19 daga wasa 22 da suka fafata a dukkan karawa.

Haka kuma Newcastle ta kasa zura kwallo a ragar Arsenal a wasa takwas daga tara da suka hadu, tun bayan nasarar da ta doke Gunners 2-0 a 2022.

Newcastle za ta je gidan Borussia Dortmund a wasan gaba a Champions League, ita kuwa Arsenal za ta karbi bakuncin Sevilla ne.

Arsenal mai maki 24 ta yi nasara a wasa bakwai a Premier League da canjaras uku, yanzu Newcastle ta doke ta.

Kawo yanzu Tottenham ce kadai ba a doke ba a bana, wadda za ta buga karashen wasan mako na 11 a Premier League da karbar bakuncin Chelsea ranar Litinin.