Amurka ta kawo karshen annobar Korona - Biden

An wallafa

Shugaba Joe Biden ya ayyana kawo karshen annobar korona a Amurka duk da cewa ana ci gaba da samun karuwar wadanda cutar ke kashewa.

Mr Biden ya ce duk da cewa har yanzu akwai matsalar, amma kuma ya ce yanayin na ci gaba da inganta sosai.

Kididdiga ta nuna cewa sama da Amurkawa akalla 400 ne ke mutuwa a sanadiyyar cutar a kowace rana.

Daman a makon da ya gabata shugaban hukumar lafiya ta duniya ya ce ana tsinkayen karshen annobar.

A wata hira da aka yi da shi da CBS wadda aka sanya ranar Lahadi, Mr Biden ya ce har yanzu Amurka na aiki tukuru domin shawo kan annobar.

A tattaunawar Shugaban ya nuna alama cewa, ''Idan kuka ga ba wanda yake sanye da takunkumi, to ku san cewa kusan kowa na cikin kyakkyawan yanayi. Ina ganin abin na sauyawa.''

Sai dai kuma jami'an gwamnatinsa gwamnatinsa sun gaya wa kafofin watsa labarai na Amurka a jiya Litinin cewa, kalaman shugaban ba suna nufin kawo sauyi a manufar Amurka ba dangane da annobar.

Kuma babu wani shiri zuwa yanzu na dage matakan gaggawa na yaki na annobar ta Covid-19.

Tun watan Janairu na 2020 zuwa 13 ga watan Oktoba kan yaki da annobar.

Zuwa yau Amurkawa sama da miliyan daya ne cutar ta korona ta hallaka.

Alkaluma daga Jami'ar Johns Hopkins na nuna cewa akalla yawan mutanen da ake samu sun mutu a sanadiyyar cutar a cikin kowane kwana bakwai har yanzu ya kai sama da 400, inda ko a makon da ya gabata sama da mutum 3,000 ne suka mutu.

A watan Janairu na 2021, idan aka kwatanta sama da mutum dubu 23 ne aka bayar da rahoton mutuwarsu a tsawon mako daya kawai.

An yi kiyasi kusan kashi 65 cikin dari na al'ummar Amurka gaba daya an yi musu cikakken riga-kafin cutar.

Har yanzu akwai wasu daga cikin dokokin da gwamntin tarayyar kasar ta bullo da su dangane da yaki da cutar.

Ciki har da tabbatar da yi wa jami'ai wadanda suka hada da ma'aikatan lafiya da sojoji allurar riga-kafi da wasu daga cikin wadanda ba 'yan kasar ba da ke shiga cikin kasar ta jirgin sama.

Manyan 'yan jam'iyyar Republican sun soki shugaban kan kalaman nasa inda tsohon Sakataren Waje na kasar Mike Pompeo ya sanya wani sakon Twitter inda yake cewa:

"Biden yanzu ya ce annobar ta kare, yayin da yake fitar da dubban sojoji masu lafiya daga cikin aikin da dokarsa ta tilasta yin riga-kafi.''

Jami'an lafiya sun bayyana kwarin guiwa amma tare da gargadi a 'yan makonnin nan cewa duniya na gabar farfadowa daga illar annobar.

Amma kuma sun ci gaba da shawartar jama'a da su ci gaba da taka tsantsan.

A ranar Litinin shugaban cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa a Amurka Dr Anthony Fauci, ya ce lalle kam lamarin ya inganta.

Amma a kalaman da ya yi a kwamtin masana na Amurka a Washington DC, likitan ya ce yawan alkaluman mutanen da ke mutuwa a sanadiyyar cutar abu ne da ba za a lamunta da shi ba.

Ya ce ba mu kai inda ya kamata mu kai ba idan har za mu ci gaba da rayuwa da cutar.

Haka kuma ya yi gargadin cewa za a iya samun sabbin nau'ukan cutar ta Covid-19 musamman a watannin da ke tafe.

A kwanan nan Amurka ta bayar da damar amfani da sabbin alluran rigakafin da suka dace da kwayar cutar nau'in wadda ta fi yawa a kasar.

Inda hukumomin lafiya suka bukaci jama'a da su tabbatar an yi musu rigakafin da ya kamata.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce duniya ba ta taba samun kanta a yanayi na kawo karshen annobar ba fiye da a yanzu.

Tare da gargadin cewa amma dai har yanzu ba a kai ga ganin bayanta ba.

Musammanonan a fannin tattalin arziki inda a makon da ya gabata kididdiga ta nuna cutukan da ke da laka da annobar ta korona na haddasa raguwar ma'aikan Amurka da kusan 500,000.

Mr Biden ya ce ya yi amanna annobar ta shafi yanayin Amurkawa matuka gaya.

Ya ce ta sauya komai halayyar mutane a kan kansu da iyalansu da yanayin kasar da kuma matsayin al'ummarsu.

Ya ce lokaci ne da ya kasance mai wuyar gaske, inda mutane sama da miliyan 6 da rabi suka mutu tun farkon bayyanar annobar a fadin duniya.

Amurka ce ta fi yawan wadanda suka mutu a sanadiyyar cutar sai kuma India sai kuma Brazil.