Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd da Erik ten Hag za su raba gari, Guehi na son tafiya Liverpool
Kociyan Manchester United Erik ten Hag na dab da shirin rasa aikinsa, yayin da ƙungiyar ta fara neman wanda zai maye gurbinsa (Teamtalk)
Shi kuwa tsohon kociyan Manchester United ɗin Ole Gunnar Solskjaer, a shirye yake ya koma idan ƙungiyar ta Old Trafford ta nemi ya nemi ya koma aikinsa. (ESPN)
Ɗan bayan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi, mai shekara 24, ba zai yi wata-wata ba idan ya samu damar tafiya Liverpool zai tafi, amma ba Newcastle wadda ta daɗe tana sonshi ba. (Football Insider)
Liverpool ba ta da sha'awar kashe fam miliyan 100 wajen sayen ɗan wasan tsakiya na Bayer Leverkusen da Jamus Florian Wirtz, mai shekara 21. (Echo)
Newcastle na faman samun cigaba a tattaunawar kwantiragi da ɗan wasan gaba na gefe na Ingila Anthony Gordon, mai shekara 23 wanda a bazarar da ta wuce Liverpool ke nemanshi. (Telegraph)
Da Liverpool ta taimaka wajen samar da kuɗin sayen Gordon ta hanyar sayar wa Newcastle da ɗan bayan Ingila Joe Gomez, a wani cinikin na daban na fam miliyan 45. (Mirror)
Newcastle na son kulla yarjejeniya mai tsawo da Gordon, wanda ita ma Arsenal ke matuƙar son tsohon ɗan wasan na Everton. (Sun)
Abin da Trent Alexander-Arnold zai fi son yi shi ne ya kulla sabon kwantiragi da Liverpool idan kwantiraginsa na yanzu ya ƙare a bazara mai zuwa. (Football Insider)
Chelsea ta yi yunƙuri da dama na sayen mai tsaron ragar AC Milan da Faransa a bazara, Mike Maignan, mai shekara 29, to amma farashin da ƙungiyar ta Serie A ta yi masa na yuro miliyan 80 shi ne ke sa Chelsean ta haƙura. (Corriere dello Sport, daga Metro)
Real Madrid na sa ido a kan ƙwazon Nico Paz a Como kuma wataƙila ta sake dawo da ɗan wasan na tawagar Argentina mai shekara 20 idan har ya ci gaba da ƙwazo a ƙungiyar ta Serie A. (AS - in Spanish)
Sean Dyche ya nuna ƙarara cewa yana son ci gaba da zama kociyan Everton, bayan saye ƙungiyar - inda zai so ya ci gaba da jagorantarsu a sabon dilin wasasu, (Telegraph)