Hukumar ƙwallon Ingila na tuhumar Osmajic da cizo ana tsaka da wasa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila (FA) ta tuhumi ɗanwasan gaba na Preston North End Milutin Osmajic da haddasa tashin hankali bayan an zarge shi da cizon ɗanwasan baya na Blackburn Rovers, Owen Beck.

Beck da yaje wasan aro daga Liverpool, an kore shi ne saura mintuna kaɗan a tashi daga wasan ranar Lahadi na hamayya saboda dukan Duane Holmes na Prestone.

Daga nan ne kuma aka fara hatsaniya, inda Beck mai shekara 22 ya yi wa lafari ƙorafin cewa Osmajic ya cije shi.

Bidiyon da aka maimaita daga baya ya nuna Osmajic yana cizon Beck a baya.

An bai wa Osmajic nan da ranar Litinin, 30 ga watan Satumba don kare kan sa, a cewar FA.

Lokacin da Luis Suarez ke taka wa Liverpool leda a 2013, an dakatar da shi tsawon wasa 10 sakaamakon cizon ɗanwasan Chelsea Brainslav Ivanovic.

Kocin Blackburn John Eustace ya faɗa wa BBC cewa: "An ji wa Owen babban rauni a bayansa saboda cizo amma abin kunya a ce lafarin bai gani ba."