Forest ta kwaso maki uku a Man United a Premier League

Ruben Amorim

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United ta yi rashin nasara 3-2 a hannun Nottingham Forest a Premier League da suka kara ranar Asabar a Old Trafford.

Forest ta ci ƙwallayen ta hannun Milenković da Gibbs-White da kuma Wood.

Ita kuwa United mai masaukin baƙi ta zare biyu ne ta hannun Hojlund da kuma Bruno Fernandes.

Da wannan sakamakon Forest ta koma ta biyar ɗin teburin Premier League da maki 25 da tazarar biyu tsakani da Manchester City, wadda ta tashi 2-2 a gidan Crystal Palace.

Ita kuwa United ta yi kasa zuwa mataki na 13 da maki 19, bayan nasara biyar da canjaras huɗuu aka doke ta karo shida, bayan wasannin mako na 15.

Wannan babbar nasara ce ga Forest, wadda ta je ta ci Liverpool a Anfield a kakar nan, yanzu kuma ta doke Man United a Old Trafford.

Wannan shi ne karo na biyu a jere da sabon kociya, Ruben Amorim ya yi rashin nasara a Premier, bayan doke shi 2-0 a Arsenal ranar Laraba.

Wannan shi ne karo na biyu da kociyan ya sha kashi a wasa biyu a jere tun bayan da ya fara horar da tamaula a tarihi.

Kawo yanzu Amorim ya ja ragamar karawa huɗu a Premier League, wanda ya ci wasa ɗaya da canjaras ɗaya da rashin nasara biyu.

Karon farko da Amorim ya yi rashin nasara a gida tun bayan Fabrairun 2023 lokacin da yake jan ragamarr Sporting, wadda Porto ta doke ta 2-1 a lokacin.

Tun daga lokacin ya yi ci wasa 23 kenan, sai doke shi da Forest ta yi ranar Asabar a Old Trafford.

Wasan da aka buga a bara tsakanin Man United da Forest:

English FA Cup Laraba 28 ga watan Fabrairu 2024

  • Nottm Forest 0 - 1 Man Utd

Premier League Asabar 30 ga wwatan Disamba 2023

  • Nottm Forest 2 - 1 Man Utd

Premier League Asabar 26 ga watan Agusta 2023

  • Man Utd 3 - 2 Nottm Forest

Ranar Alhamis United za ta buga Europa League, inda za ta je gidan Viktoria Plzen daga nan ta kara da Manchester City a Premier League a Etihad ranar Lahadi 15 ga watan Disamba.