Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutumin kogo da ya rage shi kaɗai a ƙabilarsa ya mutu a Brazil
Hukumomi sun bayya mutuwar mutum daya tilo da ya rage a zuriyar ‘yan asalin wata kabila a Brazil.
Mutumin wanda ba a san sunansa ba, ya shafe shekara 26 shi kadai cikin kadaici ya yi fice da sunan "Mutumin rami" saboda ramukan da ya haƙa masu zurfin gaske da yake kama dabbobi ko ɓuya a ciki.
An bayyana ganin gawarsa ranar 23 ga watan Agusta, a wajen bukkarsa. Babu wata alama da ta nuna kashe shi aka yi sanadin tashin hanklai.
Mutumin shi ne kadai ya rage cikin mutum shida da suka rage a zuriya da ƙabilarsu, bayan kisan da aka yi wa danginsu a shekarar 1995. Yana kuma zaune a yankin Tanaru, da ke jihar Randomnia mai iyaka da Bolivia.
Yawancin ‘yan kabilarsu, an kasha su ne tun farkon shekarun 1970, lokacin da masu kiwon dawakai suka ƙwace musu gonaki.
An yi amanna "Mutumin rami" ya kai shekaru 60 a duniya, kuma ya mutu salin-alin ba tare da wata cuta ba.
Babu wata alama da ta nuna a wurin da yake zaune, ko cikin bukkarsa, kamar yadda jami’ai suka bayyana amma dai ‘yan sanda na gudanar da bincike.
Karkashin kundin tsarin mulkin Brazil, ‘yan asalin kasa na da hakki kan filayensu, an yi amanna wadanda suka raba su da filayen kashe su suka yi.
Jami’an sirri na kabilu ‘yan asalin Brazil (Funai) sun dade suna sanya ido kan "Mutumin rami" domin ba shi kariya tun shekarar 1996.
A shekarar 2018, mabobin Funai, sun yi nasarar daukar bidiyon mutumin a cikin daji. A bidiyon an gan shi ya na kokarin hawa bishiri da wani abu da ya yi kama da gatari.