Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka kama likitan da ke yi wa mata fyade yayin yi musu tiyatar haihuwa
'Yan sanda a birnin Rio De Janeiro na kasar Brazil sun kama wani likita bayan da kyamara ta dauke shi yana yi wa wata mai jego fyade a lokacin da take tsaka da radadin haihuwa.
Rahotonni sun ce Bidiyon ya nuna yadda likitan mai suna Giovanni Quintella Bezerra, ke kokarin sanya gabansa cikin bakin matar jim kadan bayan likitoci sun yi nasarar cire mata jariri.
Giovanni Quintella Bezerra likita ne, da ke yi majinyata allurar kashe radadi kafin yi musu tiyata.
Majiyoyi sun ce likitan ya goge bakin matar da tolifefa bayan da ya kammala, saboda kar mutane su fahimci abin da ya aikata.
Lamarin ya faru jim kadan bayan mijin mai jegon ya fice daga dakin haihuwar dauke da jaririn.
Jami'an asibitin ne suka sanya kamera a dakin tiyatar, a lokacin da za a yi wa matar tiyata, bayan da suka yi zargin cewa allurar bacin da ake yi wa marasa lafiya a lokacin tiyata na yin yawa.
An kama likitan, mai shekara 32, bisa zargin yi wa mai jegon allurar barcin da ta wuce kima, domin aiwatar da abin da ya yi.
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
Wasu mutane sun yi korafi
Kafar yada labbaran kasar Globo, ta ruwaito wani mutum na cewa Likita Bezerra ya taba ce masa ya fice daga dakin tiyata inda matarsa ke kwance, ficewarsa ke da wuya ya yi mata fyade.
''Na je domin ganin jaririn sai likitan ya ce min in fita daga dakin, a lokacin kuma matar tawa na bacci ba ta farfado ba'', In ji mijin matar.
Ya ce ya gane fuskar likitan ne a lokacin da ya ganshi a talabijin.
Hukumomin lafiyar kasar sun yi Allah wadai da lamarin, kuma tuni suka fitar da wata sanarwa da ke cewa sun mika batun wajen 'yan sanda domin gudanar da bincike, kuma za su dauki matakin da ya dace a kan likitan.
Idan aka tabbatar da laifin kan likitan zai iya fuskantar hukuncin daurin shakara 15 a gidan yari.