Neymar ya zama na hudu a yawan ci wa PSG kwallaye

An wallafa

Dan wasan Brazil, Neymar ya zama na hudu a yawan ci wa Paris St-Germain kwallaye a tarihi.

Ranar Asabar PSG ta doke Brest 1-0 a wasan mako na bakwai a gasar Ligue 1.

Mai shekara 30 ne ya ci kwallon kuma na 110 kenan, ya haura matakin tsohon dan wasan tawagar Portugal, Pauleta a yawan ci wa PSG kwallaye.

Lionel Messi ne ya bai wa Neymar kwallon da ya zura a raga na takwas a kakar nan a wasa na bakwai a babbar gasar tamaula ta Faransa.

Edison Cabani ne kan gaba a yawan ci wa PSG kwallaye a tarihi, sai Zlatan Ibrahimovic na biyu mai 156, sannan Kylian Mbappe na uku mai 180.

Ana tsaka da wasa aka bai wa dan wasan Brest, Christophe Herelle jan kati, sakamakon ketar da ya yi wa Neymar daga baya aka soke, bayan da VAR ta fayyace cewar dan wasan PSG ya yi satar gida kafin ketar da aka yi masa.

Messi da Mbappe duk sun samu damarmaki da yawa, sai dai ba su zura kwallo ba a raga a fafatawar.