Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya janyo rikicin Hausawa da 'yan kabilar Berta a kasar Sudan
Bukatar da al’ummar Hausawa a Sudan suka nema ta a ba su ‘yancin mallakar wasu wurare a jihar Blue Nile ta yi sanadin barkewar kazamin rikici.
A makon jiya, rikici ya barke tsakanin kabilar Berta da take bayyana kanta a matsayin ‘yan asalin yankin da kuma Hausawa.
Sama da mutum 100 aka kashe sannan aka tilasta wa dubban Hausawa tserewa daga gidajensu, lamarin da ya janyo gagarumar zanga-zanga a wani bangare na Sudan kan musguna wa Hausawan.
Akalla mutum takwas ne suka mutu bayan wannan zanga-zanga a baya da ‘yan sanda suka yi kokarin dakatarwa.
Su waye al’ummar Hausawan?
Hausawan da asalin tushensu ya fito daga yammacin Afirka, sun kwashe karni da yawa suna rayuwa a Sudan — galibi suna zama a kasar ne a matsayin zango— yayin da suke doguwar tafiya mai cike da wahala ko zuwa Makka domin aikin Hajji.
Dukkan Musulmi kan yi kokarin ziyartar kasa mai tsarki akalla sau daya a rayuwa domin yin aikin Hajji.
Turawan mulkin mallaka a Najeriya na cikin mutanen da suka sanya tafiye-tafiyen Hausawa zuwa Gabas ta Tsakiya lokacin da suka ci galaba kan Daular Usmaniyya a 1903, inda jikoki da mabiyansa da dama suka koma da zama a Sudan.
A yau, al’ummar Hausawa sun warwatsu ta ko’ina a duniya. Bayan samun ‘yanci a 1956, an yi kiyasin cewa akwai Hausawa 500,000 – sannan a yanzu sun kai miliyan 3 zuwa miliyan 10 cikin miliyan 44 na al’ummar Sudan.
Suna rayuwa ne tare da aiki a tsakiyar Sudan a ma’aikatun harkokin aikin gona da gonaki da ke Kogin Sudan – sai dai yawancin biranen kasar na da al’ummar Hausawa.
Tasirinsu kan al’adun ‘yan Sudan ba zai misaltu ba – kuma ana ganin haka a wuraren jama’a kamar kasuwanni da gidajen sayar da abinci.
Duka wannan, saboda abincinsu na Agashe na cikin abinci da aka fi so: nama da ganyayyaki da naman kaza da wasu nau’ukan abinci da abin sha.
Aisha al-Falatiya ita ce mace ta farko da ta fara waka a wani gidan rediyo a Sudan a 1942, mawakiya ce da ta shahara a Sudan saboda wakokinta na soyayya da take yi da Hausa – da sauran wakokinta na siyasa, musamman gabanin samun yanci.
Ta kuma ziyarci nahiyar Afirka lokacin Yakin Duniya na Biyu, inda ta nishadantar da dakarun Sudan da ke taimakawa Birtaniya a yakin.
Duk da haka, Hausawa na shan wahala wajen karbuwa a wajen al’ummomin Sudan.
"Hausawa sun dade suna fuskantar tashin hankali…sannan sun gaji da kiransu a matsayin ‘yan kasashen waje,’’ a cewar wani mai bincike Mohamed Ali, wanda kuma masani ne kan al’ummomi a Sudan da kasashe da take hulda da su a Afirka ta Yamma.
Me ya sa ake samun tashin hankali?
Tashin hankalin na da alaka da filaye.
Lokacin mulkin mallaka, Birtaniya ta kirkiro da wani tsarin noman rani mafi girma a duniya tsakanin jihohin Blue Nile da White Nile.
Lokacin da tsarin ya soma a 1911, an fi amfani da bayi a matsayin leburori domin noman auduga wa masana’antun arewa maso yammacin Ingila.
Bayan da Birtaniya ta kawo karshen sana’ar bayi a yankin a 1924, yankin Gezira, da a yau ya fadada zuwa sama da eka miliyan 2 – na fama da karancin ma’aikata.
A cewar Mr Ahmed, mafita daya da turawan mulkin mallaka suka kawo ita ce bai wa al’ummar Hausawa 3,000 filaye domin karfafa musu gwuiwar zama a wajen – inda yawancinsu ke aiki da tsarin noma a Gezira.
Wannan ya sanya Hausawa da yawa samun wuraren zama na dindindin. Sai dai tun da fari, wasu mazauna yankin ba su ji dajin hakan ba sannan sun ce bai wa al’ummar Hausawa da ke tasowa filaye ba daidai ba ne.
Wannan ya biyo bayan dokar takaita ba da izinin zama dan kasa a shekarar 1948.
"An ki bai wa Hausawa shaidar zama dan kasa saboda su ba ‘yan asalin Sudan ba ne a cewar hukumomi da hadin gwuiwar gwamnatin Birtaniya, wanda kuma ya sanya aka hana su damar yin karatu da sauran wasu damar-maki,’’ a cewar Mr Ahmed.
Shekara 8 bayan samun 'yancin Sudan, babu wani sauyi na a zo a gani – ta yadda sai mutum ya nuna cewa kakan-kansa dan Sudan ne kafin samun shaidar zama dan kasa, abu kuma da ya zama mai wahala ga Hausawa.
Hakan ya sauya a 1994 lokacin da dan siyasa mai akidar Musulunci, Hassan Turabi ya zama kakakin majalisar kasar, inda ya kawo dokar da ta bai wadanda aka haifa a Sudan ko suka yi rayuwa na shekara 5 'yancin zama ‘yan kasa.
Sai dai Mr Ahmed ya ce Hausawa na ci gaba da fuskantar bambanci daga jami’ai, inda ta kai sai Bahaushe ya kawo shaidu guda hudu da za su yi rantsuwa cewa shi dan Sudan ne – wanda hakan ke ba su wahala wajen samun takardu.
Rikicin makon da ya gabata ba shi ne na farko da suka taba fuskanta ba. Dalibai sun gudanar da zanga-zanga a Khartoum, babban birnin Sudan, kan yarjejeniyar kawo karshen yakin basasa a kudancin kasar da ya kazanta a 1974.
Daya daga cikin wadanda ‘yan sanda suka kashe yaro ne da ya fito daga al’umma da ake dangantawa a Afirka ta Yamma.
Hakan ya sanya hukumomi hakikance cewa wadannan al’ummomi, hade da Hausawa na da hannu a zanga-zangar ta adawa – sannan an haramtawa wasu daga cikinsu shiga biranen Khartoum da Omdurman.
A cewar Mokhtar Ali, wani Bahaushe mazaunin birnin Omdurman a lokacin, ya ce an hari kan mutane da ake dauka ‘yan kasashen waje a garuruwa da dama da ke wajen birnin.
Inda aka sanya wasu daga cikinsu cikin jiragen kasa zuwa Nyala a kudancin Darfur da kuma cikin manyan motocin safa-safa zuwa Adre da ke gabashin Chadi.
Sai dai gwamnatin Chadi, ta ki bari su wuce, wand ya janyo al’ummar Hausawa suga samu matsugunai a Darfur da wasu sassan Sudan.
Rikici ya sake barkewa a watan Oktoban 2008 lokacin da shugaba Omar al-Bashir ke mulki. Wata jarida ta ruwaito shi yana cewa al’ummar Hausawa ba ‘yan asalin Sudan ba ne.
Hakan ya janyo zanga-zanga, inda mutane bakwai suka mutu sannan aka raunata sama da 100.
Amma Shugaba Al-Bashir ya musanta furta kalaman.
Me ya janyo sabon rikicin?
Abin na da sarkakiya – sai dai ana danganta mafarin rikicin kan mallakar filaye hade da rikice-rikice na siyasa na son iko da jihar ta Blue Nile.
A wata da ya gabata, sabon gwamnan jihar Blue Nile, ya amince da bukatar Hausawa na kafa masarautar su a jihar, wanda ya bai wa Hausawan damar fada a ji kan harkokin cikin gida.
Hakan ya bata wa shugaban sarakunan jihar rai, wanda ya fito daga kabilar Berta – da kuma ya bada shawarar cewa kada a bawa Hausawa iko sosai, inda maimakon haka ya ce a nada shugabansu a matsayin babban malami.
Wannan ya jawo kiraye-kiraye daga kafafen sada zumunta na cewa a kwashe izinin zama dan kas ana al’ummar Hausawa da kuma filayensu na noma.
An kuma yi garkuwa da sabon sarkin na Hausawa wanda hakan ya janyo tashin hankali na baya bayan -nan.
Masu sa ido sun ce dukkan bangarorin na samun goyon baya daga wajen wasu bangarori na jam’iyyar SPLM N na jihar Blue Nile – Wani bangare ya amince ya mika makamansa, sai dai dayan bangaren sun ki amincewa su mika nasu.
Sabani na jam’iyyar SPLM-N ya bar al’ummar Hausawa da zimmar ganin gwamnan jihar ya cika alkawarinsa na kirkiro musu masarautar su.
Rabe-raben kawunan zai iya shafar dakarun kasar – wanda hakan zai sanya su karfafa gwuiwar wasu kan rikicin.
Akwai fargabar cewa zasu kau da kai daga zanga-zangar adawa ake ci gaba da yi a fadin kasar kan juyin mulki a watan Oktoban da ya gabata, lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin hadaka da kungiyoyin fararen hula da ke da niyyar shirya zabuka a shekara mai zuwa.