Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
‘Na kwashe watanni ban ci nama ba, amma duk da haka ba zan sayar da mutuncina ba’
- Marubuci, Fundanur Öztürk
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Turkish
- Aiko rahoto daga, Ankara
- An wallafa
Tulane, mai 'ya'ya shida, ta ce ba za ta koma Syri'a ba, duk kuwa da fama da cin zarafin lalata da matsin tattalin arziki da take fuskanta a Turkiyya, inda take zaune a yanzu.
A lokacin da take gida Syria ta kasance malamar makaranta, amma a yanzu, sana'ar sayar da abinci take yi, inda take samun dala 220 a wata, kusan rabin mafi ƙarancin albashi da ake biya a Turkiyya, wato dala 420 a wata.
Tulane(ba sunanta na gaskiya ba), mai shekara 42, ta ce mijinta ba zai iya jure wa wahalar yanayin rayuwa da ake fama da ita a sansanonin 'yan gudun hijira a Turkiyya ba. A don haka ne ya koma Syria shekara biyu da suka gabata, inda ya bar ta tare da 'ya'yansu.
Daga nan ne rayuwarta ta shiga tangal-tangal, kamar yadda ta shaida wa BBC.
Maza kan je wajenta da nufin taimaka mata ko samar mata da aiki, amma idan suka fahimci ba ta da miji, sai su riƙa 'neman ta', ko su nemi 'ya'yanta.
"Akwai lokacin da ubangidana a aiki ya kama hanuna, sai na fincike na gudu. Suna tunanin za mu sayar da kanmu a kan abincin, Na kwashe watanni ba tare da cin nama ba, amma duk da haka ba zan sayar da mutuncina ba", in ji ta.
Mijin Tulane ya sake yin wani auren bayan ya koma Syria, kuma ya ci gaba da gudanar da rayuwarsa.
"Idan na koma Syria, ilimin 'ya'yana zai taɓarɓare. Don haka dole na jure wa yunwa, da cin zarafi, da ƙyamar baƙi da ake nuna mana, domin kuwa ba zan koma gida ba," in ji Tulane.
'Yan Syria fiye da mutum miliyan 3.3 ne ke zaman gudun hijira a Turkiyya, lamarin da ya sa ta zama ƙasar da ta fi kowacce ƙasa yawan 'yan gudun hijira a duniya.
Galibin mutanen kan yi aiki a kamfanonin masaƙu, da gonaki, da wuraren sayar da abinci, da ɓangaren gine-gine.
Kusan 'yan gudun hijirar Syria miliyan guda ne aka ƙiyasta cewa suna aiki ba tare da takardun izini ba a Turkiyya. Hakan na nufin ba su da damar samun haƙoƙokin tsaro da walwala, ko mafi ƙarancin albashi kamar yadda doka ta tanada ba.
Dokar aikin gwamnati a Turkiyya ta tanadi cewa, idan za a ɗauki ma'aikata 'yan ƙasasashen waje dole a biya su ninki uku na mafi ƙarancin albashi.
Hakan ne ya sa mafi yawan masu ɗaukar aiki, ke ɗaukar mutanen da ba su da takardun izini aiki, domin su biya su ƙasa da abin da doka ta tanada.
Alƙaluman hukuma sun nuna cewa matan Syria 5,000 ne kawai suke da takardun izinin aiki a Turkiyya.
Yayin da hauhawar farashi ta kai kashi 56, tare da fama da tsadar rayuwa a ƙasar, matan Syria na cewa dole ne su jure wa cin zarafin lalata domin riƙe ayyukansu.
Lamya ta kai mu wani lalataccen gini wanda take rayuwa a cikinsa, da shigar mu, muka ci karo da wani mugun wari da ke tasowa daga cikin gidan.
Matar, mai 'yaya biyar, ta shaida wa BBC cewa dole ce ta sanya take rayuwa a wanna gida, saboda tsohon gidanta ya kasance tamkar 'bariki', domin kuwa har 'gidan mata' ake kiran sa.
"Bana iya bacci da daddare, saboda kare 'ya'yana. Na shiga tsoro da razani, don haka na ɗauki matakin barin gidan tare da komowa nan', in ji matar mai shekara 38.
Lamya - wadda ba sunanta ne na gaskiya ba - ta ce tana yawan fama da matsalar cin zarafi a wurin aikinta.
"Idan ke bazarwa ce, ko ba ki da miji, duka idon mutane na kanki, za su riƙa bin ki a koyaushe'.
Idan ke bazawara ce a wurin aiki, kin zama tamkar wata karya a wajen maza, za su riƙa bibiyarki da farko da nufin taimaka miki ta hanyar samar miki da aiki, daga nan sai su zo da buƙatarsu a gare ki.
"Na ƙi gaya wa kowa a wurin aiki cewa ba ni da miji. A baya oganmu wurin aiki da ya fahimci ba ni da miji, sai ya fara bibiyata tare da yawan kira na a yawa, don haka dole na bar wanan aiki".
A wani gidan da ke makwabtaka da ita, wasu mata biyu iyaye, marasa aure ne ke zaune tare da juna don rage wa juna tsadar kuɗin da za a biya.
Ranar aiki a kamfanin masaƙa, kuma ba ta da takardar izinin aiki a ƙasar, lamarin da ya sa take karɓar ƙasa da mafi ƙarancin albashi a Turkiyya.
Yousra kan zauna a gida domin kula da 'ya'yan hudu da mahaifiyarsu wadda ta tsufa.
Sun ce ana cin zarafinsu ta hanyar lalata, tare da nuna musu ƙyamar baƙi a wuraren da suke aiki, da kuma cikin gari, tare da tsangwamar su saboda kasancewar suna da 'ya'ya amma ba su da miji.
Kasancewar sun je Turkiyya cike da fata, Rana ta ce ba ta hango wa 'ya'yanta makoma mai kyau.
"Duk kuɗin da muka samu yana tafiya ne wajen biyan kudin haya da sauran abubuwa. Yunwa na damun mu a koyaushe, bugu da ƙari kowa a cikin gari na nuna mana ƙyama," in ji ta.
Lamya ta kuma yi ƙorafi kan wariya da ake nuna musu, duk kuwa da shafe shekara fiye da 10 a Turkiyya.
"Wata rana muna zaune a kan kujera, wasu matan Turkiyya biyu suka fara yi mana tsawa, suna cewa 'yaushe za ku koma Syria?' suna yawan yi mana ihu," in ji ta.
"A yanzu mafarkin da nake yi, shi ne na tafiya Turai. Wannan shi ne burina dare da rana."