Ruben Loftus-Cheek: Ɗan wasan Chelsea na dab da komawa AC Milan

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, g
An wallafa

Ɗan wasan tsakiya na Chelsea Ruben Loftus-Cheek na dab da komawa ƙungiyar AC Milan ta Italiya.

Matashin ɗan wasan mai shekara 27 wanda ya bugawa Ingila wasa 10, ya samu kansa a Stamford Bridge tun yana yarinta, ya je wasan aro a Crystal Palace da Fulham.

A lokacin da yake Chelsea ya lashe Premier biyu, da Fifa Club World Cup da Uefa Supercup.

'Yan wasa da dama sun bar ƙungiyar Chelsea a wannan kakar, a wani mataki na daidaita tsarin 'yan wasanta.

A ranar Lahadi ne aka kammala cinikin ɗan wasan Senegal Kalidou Koulibaly wanda ya koma Al-Hilal ta Saudiyya.

Shi ma N'Golo Kante ya sanya hannu domin komawa ƙungiyar Al-Ittihad wanda ta lashe gasar Saudiyya, yayinda abokin wasansa Edouard Mendy ke dab da komawa Al-Hilal.

Ɗan wasan ƙungiyar na tsakiya Meson Mount na da shirin komawa Manchester United, wanda ta taya shi sau uku ba a taya ba.

Ɗan ƙasar Jamus ma Kai Havert shi ma na dab da komawa Arsenal.