Europa League: Salah ya shirya buga wasan Sparta Prague

Asalin hoton, PA Media
Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce Mohamed Salah a shirye yake ya buga wasan da za su karbi bakunci Sparta Prague a Europa League zagayen 'yan 16 ranar Alhamis.
Har yanzu Liverpool ba ta fara wasa da Salah ba tun daga 1 ga watan janairu, bayan raunin da ya ji a lokacin da yake buga wa Masar gasar kofin nahiyar Afirka a Ivory Coast.
Liverpool ta yi nasarar cin 5-1 a wasan farko zagayen 'yan 16 a Jamhuriyar Czech ranar Alhamis 7 ga watan Maris.
''Ban sani ba ko zai iya buga minti 90, amma dai na san ya shirya yin fafatawar'' in ji Klopp.
''Ya kamata a fara wasa da shi a karawar da muka tashi 1-1 da Manchester City a Premier League a Anfield, amma mun barshi ya huta sosai kada a samu matsala.''
''Saura wasa 10 a kammala Premier League ga kuma sauran fafatawar Europa League da FA Cup, dukkansu suna da mahimmanci.''
Salah shi ne kan gaba a yawan ci wa Liverpool kwallaye a bana, mai 19 a raga, amma ya ji rauni a wasan Masar da Ghana da suka tashi 2-2 cikin Janairu a Ivory Coast.
Ya canji dan wasa a karawar da Liverpool ta ci Brentford 4-1 ranar 17 ga watan Fabrairu har ma ya zura kwallo daya daga ciki.
Daga nan kuma bai samu buga wasa hudu ba har da wanda Liverpool ta lashe Carabao Cup na bana, bayan nasara a kan Chelsea a bugun fenariti.
Salah ya shiga wasa daga baya a fafatawar farko a Sparta Prague da Liverpool ta yi nasarar cin 5-1, wanda ya yi mata minti 16.
Wadanda suka ci wa Liverpool kwallayen sun hada da Darwin Nunez da ya zura biyu a raga da Alexis Mac Allister da Luis Diaz da kuma Dominik Szoboszlai.
Liverpool tana ta biyu a teburin Premier League da maki iri daya da na Arsenal ta daya, za ta buga kwata fainals a FA Cup, bayan da ta lashe Carabao Cup a bana.
To sai dai kuma a karshen kakar bana Jurgen Klopp zai bar Liverpool, kamar yadda ya sanar yana son ya huta tare da iyalansa.











