Lewandowski ya ci kwallo na 12 a wasan da Barca ta ci Bilbao

Robert Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Robert Lewandowski ya ci kwallo na 12 a wasa 11 a La Liga, bayan da Barcelona ta doke Athletic Bilbao 4-0 a ranar Lahadi a Nou Camp.

Dan wasan tawagar Poland shi ne ya ci na uku, bayan da ya samu kwallo daga wajen Ousmane Dembele.

Tun farko Lewandowski ne ya bai wa Dembele kwallon farko da Barcelona ta fara zurawa a raga a karawar mako na 11 a gasar La Liga.

Dembele shi ne ya bai wa Sergi Roberto, wanda ya zura na biyu a raga, haka kuma dan wasan Faransa shi ne dai ya bai wa Ferran Torres ya ci na hudu.

Nasarar ta bai wa Barcelona maki ukun da take bukata, sai dai kuma Roberto ya ji rauni a allon kafata a wasan na babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

To sai dai Real Madrid mai maki 31 daga wasa 11 tana ta dayan teburin La Liga, ita kuwa Barcelona tana ta biyu da tazarar maki uku, bayan yawa wasa iri daya da na Real.

Wasu batutuwan da ya kamata ku sani kan wasan Barca da Bolbao:

Robert Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona ta fuskanci tsohon kociyanta Ernesto Valverde mai jan ragamar Bilbao, wadda kawo yanzu ba a doke kungiyar ba a wasan da ta yi a waje a bana.

Sai yanzu ne Barcelona ta yi nasara a kan kungiyar a fafatawar da ta kai bakuncin a kakar nan.

Valverde ya horar da Barcelona tsakanin 2017 zuwa 2020, wanda ya lashe La Liga biyu da Copa del Rey a kungiyar ta Nou Camp.

Rabon da Athletic ta yi nasara a Nou Camp tun 2001/02 a wasa 20 da ta kai ziyara, inda Barca ta ci 17 da canjaras uku.

Canjaras na baya-bayan .nan da suka yi shi ne 1-1 a 2018 kuma a karkashin jagorancin Valverde a lokcin yana Barcelona.

2021/2022

Spanish La Liga Lahadi 27 ga watan Fabrairun 2022               

  • Barcelona         4 - 0 Ath Bilbao       

Copa del Rey Alhamis 20 ga watan Janairun 2022         

  • Ath Bilbao        3 - 2 Barcelona        

Spanish La Liga Asabar 21 ga watan Agustan 2021        

  • Ath Bilbao        1 - 1 Barcelona

'Yan wasan da Barcelona ta fuskanci Bilbao da su:

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X