Abubuwa huɗu da za su iya tantance ƙungiyar da za ta lashe Premier

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Uku daga cikin manya shida na gasar Premier sun samu sauyin sabbin masu horarswa, yayin da gwarzuwar gasar Arsenal take fama da jinyar manyan 'yan wasanta, Tottenham da Chelsea kuma sun kafa tarihi a kasuwar saye da sayerwar 'yan wasa.

Bayan shekarun da Manchester City ta kwashe na mamaye gasar sannan Liverpool ta biyo baya yanzu kuma Arsenal ta lashe ta da tazarar maki bakwai, yanzu gasar Premier ta sake faɗaɗa, ba za a iya cewa wane ne zai ci ba, ƙungiyoyi sun yi gyara.

Ga wasu dalilai huɗu da za su sanay kakar 2026/27 za ta zama mai ƙayatarwa.

Sabon sa rai kan sabbin koci

Ta ya zaka mamaye gurbin wanda ba za a iya maye gurbinsa ba?

Manchester City har yanzu suna cikin waɗanda ake sa ran za su iya ƙara cin gasar, wadda ta ci shida cikin tara da aka buga a bya, amma za su fara kakar ba na ba tare da kocinsu da ba su taɓa irinsa ba a tarihi, Pep Guardiola.

Kocin mai shekara 55 ya jagoranci City ta ci kofina 17 a shekara 10, ya ajiye aiki a kakar da ta ƙare kuma an maye gurbinsa da tsohon mataimakinsa Enzo Maresca.

Tun a watan Janairu da Maresca ya ajiye aiki ba shi da abin da yake yi.

Daga nan Chelsea suka yi sabon koci. Sun maye gurbin Maresca da Liam Rosenior daga baya suka sallame shi kafin kakar ta ƙare suka ɗauki tsohon ɗan wasan Liverpool Xabi Alonso.

Shekaru biyu da suka gabata, Alonso ya ɗauki gasar Bundesliga da ƙungiyar Bayer Leverkusen, bayan nan yaje Real Madrid amma bai cimma abin da yake so ba a can.

Da yawa sun yi tsammanin zai maye gurbin Arne Slot da ya lashe Premier a 2024/25 amma sai Reds suka ɗauki Andoni Araola da ya kammala gasar a mataki na shida da Bournemouth.

Wadannan ne manyan ƙungiyoyi uku da sabbin koci.

Sai kuma me, Kocin Manchester United da Michael Carrick da na Tottenham Roberto de Zerbi sun karɓi ƙungiyoyinsu ne daf da za a gama kakar da ta gabata.

Dan haka biyar cikin ƙungiyoyin gasar shida manya za su fara kakar mai zuwa ne da sabbin kocin da ba da su aka fara ba a bara.

Kocin Arsenla Mikel Arteta ne kawai aka ba shi aikin tun 2019, kuma har yanzu ake damawa da shi.

Rashin Saliba zai iya haifar ga koma baya ga Arsenal

A matsayinsu na masu rike da gasar da kuma kocin da ya san gasar sosai, an fi ganin Arsenal za ta iya ƙara lashe gasar a nan gaba.

Amma doguwar jinyar da wasu manyan 'yan wasanta ke fama da ita ka iya shafar damar da take da ita ta lashe kofin.

Ƙumgiyar ta ce ɗan wasanta na baya Wiliam Saliba zai yi jinya ta dogon lokaci sakamakon ciwon bayan da yake fama da shi da ya ji a Gasar Kofin Duniya da ƙasarsa Faransa.

A kakar da ta wuce ɗan wasan mai shekara 25, ya buga wa Arsenal wasanni 50 a duka gasanni, kuma shi da abokin yin bayansa Gabriel ne ba a sawa kwallaye da yawa ba agasar.

Arsenal za ta fara kakar da wasanni masu wahala, inda za ta haɗu da Aston Villa da Chelsea a wasanninta uku na farko.

Tun daga 2022 da Seliba ya fara bugawa Arsela wasa, ta ci kimanin kashi 68 na wasanninta a Premier a wasanni 131.

Amma lokacin da bai buga wasanni ba, nasarar ta ragu zuwa kashi 47.6 a wasanni 21.

Ko gasar zakarun Turai za ta kawo wa Man United tangarɗa?

A kakar bara, Manchester United wasa 40 kacal ta yi a duka kaka, shi ne mafi ƙaranci da ta taɓa yi a kaka ɗaya tun 1914-15, kuma ta kammala Premier a matsayi na uku.

Chelsea ta yi wasa 59 a duka kakar bara ta kuma kammala kakar a matsayi na 10.

Tottenham kuwa wasa 52 ta yi a duka gasa, wadda da kyar ta tsira daga faɗawa gasar Championshi mai mataki na biyu.

Buga yawan wasanni baya nufin zai sa ƙungiya ta kare kaka a ƙarshen teburi. Kamar Arsenal ta ci Premier bara kuma ta kai wasan ƙarshe na gasar Zakarun Nahiyar Turai.

Amma a wasu gasanni yawan wasanka yawan nasararka.

A bara Spurs sai da ta yi rashin 'yan wasa 27 saboda rauni da jinya da sukai ta fama da ita.

A kaka mai zuwa Chelsea da Tottenham ba za su buga kowacce gasa ta nahiyar Turai ba, yayin da a gefe kuma Manchester United da ƙungiyoyi takwas a gasar za su buga gasar turai.

Manchester United ta nuna shirinta ta yadda take fatan daukar 'yan wasan tsakiya a kasuwar 'yan wasa, inda ta sayi Andrey Santos da Youri Tielemans daga Chlesea da Aston Villa.

Amma abin tambayar shi ne ƙarin wadannan 'yan wasa zai cike giɓin wasannin da suka ƙararwa United?

Shin Chelsea da Spurs za su ba da mamaki a kaka mai zuwa

Chelsea da Tottenham ba su yi ƙoƙari ba a bara, amma dukansu za su iya ba da mamaki saboda manyan 'yan wasa da suka saya.

Chelsea ta ɗauki ɗan wasan Ingila Morgan Rogers wanda shi ne mafi tsada a tarihin 'yan wasan Burtaniy, ta saye shi £117m daga Aston Villa.

Sun kuma ƙara kashe £47m wajen sayen ɗan bayan daga Atlanta Marco Palestra kuma suna nan dab da ɗaukar Danny Welbeck da Jordan Henderson da kuma Maxence Lacroix.

Ita ma Tottenham ta kusa kashe abin da Chelsea ta kashe, tana ta ƙoƙarin kashe £237m a wannan kakar.