Sabon faɗa ya ɓarke tsakanin sojojin Habasha da mayaƙan Tigray
Rahotanni daga arewacin Habasha sun ce an sake samun sabbin faɗace-faɗace tsakanin sojojin ƙasar da mayaƙan ƙungiyar TPLF a yankin Tigray.
TPLF ta zargi gwamnatin Habasha da ƙaddamar da wani farmaki a ranar Asabar a kusa da yankin Shererina da ke makwabtaka da iyakar Sudan, inda ta ce an yi amfani da dakarun ƙasa da manyan bindigogi wajen kai harin.
Wannan shi ne sabon rikici tsakanin ɓangarorin biyu, bayan da gwamnatin da ke Addis Ababa ta zargi mayaƙan Tigray a makonnin baya da shirin sake tayar da yaƙi. Rahotanni sun nuna cewa duka ɓangarorin sun tara dakarunsu a yankunan da ke kusa da Tigray.
Har yanzu ba a san ko wannan rikicin zai rikiɗe ya zama wani sabon yaƙi mai faɗi ba.
Shugabannin Tigray dai sun ɗora laifin sabuwar takun-sakar kan gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed, suna zarginta da gaza aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2022 wadda ta kawo ƙarshen yaƙin shekara uku da ya yi sanadin mutuwar fiye da rabin miliyan mutane.