Gane Mini Hanya: Tare da Malam Ibrahim Shekarau 26/10/2024

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ana samun yunƙuri daga ƙungiyoyi da rukunin masu faɗa-a-ji da ke fitowa suna gangami da shirya taruka a kan mawuyacin halin da yankin arewacin Nijeriya ya samu kansa ciki a shekarun baya-bayan nan.

A cikin masu irin wannan yunƙuri, har da wata ƙungiya ta masu rajin farfaɗo da ruhin dimokraɗiyya a arewacin Nijeriya mai suna Northern Democrats League a ƙarƙashin tsohon gwamnan jihar Kano Mallam Ibrahim Shekarau.

Ƙungiyar wadda ta fara kai ziyara ga fitattun manyan ƴan Nijeriya, ta ce ta damu matuƙa da taɓarɓarewar al'amura a kusan dukkanin fannonin rayuwa a arewa.