Real na fatan cin Girona a La Liga ba tare da Benzema ba

La Liga

Asalin hoton, Real Madrid FC

An wallafa

Real Madrid na sa ran cin Girona a karawar mako na 31 a La Liga ranar Talata a Estadio Montilivi.

To sai dai Karim Benzema ba zai buga wasan ba, mai kwallo 14 a La Liga, wanda ya yi karawar da Real ta ci Celta 2-0 ranar 22 ga watan Afirilu.

Real Madrid da Girona sun tashi 1-1 a wasan farko a bana a La Liga ranar 30 ga watan Oktoba a Santiago Bernabeu.

Vinicius Junior ne ya fara cin kwallo a minti na 70, yayin da Girona ta farke saura minti 10 a tashi daga wasan ta hannun Cristhian Stuani a bugun fenariti.

A karawar ce aka bai wa Toni Kroos jan kati daf da za a busa tashi daga wasan.

Girona tana daga cikin kungiyoyi biyar da suka yi canjaras da Real Madrid a bana a La Liga, ciki har da Osasuna da Real Sociedad da Atletico da kuma Betis.

Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da maki 65, inda Barcelona ce ta daya mai maki 76.

Girona mai maki 38 tana ta 11 a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya, wadda ta ci karawa 10 a bana da canjaras takwas aka doke ta fafatawa 12.

Haka kuma wasa hudu kacal aka ci Girona a gida a La Liga kawo yanzu.

'Sauran 'yan kwallon da ba za su buga wa Real Madrid karawar ba sun hada da Alaba, da Mendy da Hazard da kuma Ceballos.

Alkalin wasa shine Javier Iglesias Villanueva, wanda karon farko zai busa wasan Real Madrid a kakar nan.

Wanda zai kula da VAR shine Jose Luis Gonzalez Gonzalez.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis López.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V. da kuma Rüdiger.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Mario Martín da kuma Arribas.

Masu cin kwallaye: Asensio, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.

Wasannin da za a buga ranar talata 25 ga watan Afirilu:

  • Cadiz da Osasuna
  • Girona da Real Madrid
  • Real Betis da Real Sociedad