Lewis ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Man City

Rico L;ewis

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Matashin mai tsaron bayan Manchester City, Rico Lewis ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar domin ya ci gaba da taka leda a Etihad.

Mai shekara 18 ya fara yi wa City tamuala a bara, wanda kawo ya buga karawa 16 da cin kwallo a kakar da City ta lashe kofi uku.

Tun farko saura kwantiragin kaka daya ya rage masa a City, yanzu zai ci gaba da taka ledaa Etihad zuwa karshen kakar 2028.

A cikin watan Maris, Lewis ya fara buga wa tawagar matasa ta Ingila 'yan kasa da shekara 21 tamaula.

Wasa na biyar da ya buga wa City shine karawar Champions League da Sevilla a Nuwamba, wanda ya zama matashin da ya ci kwallo a gasar.

Mai rike da tarihin bajinatar shine tsohon dan kwallon Real Madrid, Karim Benzema.

Ranar Laraba Manchester City za ta kara da Sevilla a wasan Uefa Super Cup, karawa ce tsakanin City mai rike da Champions League da Sevilla mai Europa.

Ranar Juma'a City ta doke Burnley 3-0 a wasan makon farko da fara gasar Premier League ta kakar 2023/24.