Man Utd na son Gomes, Barca za ta bai wa Everton 'yan wasa hudu a kan Onana

An wallafa

Manchester United na harin sayen dan wasan tsakiya na Wolves Joao Gomes, a matsayin wanda zai maye gurbin dan uwansa dan kasar Brazil Casemiro, 32. (Mirror)

Arsenal, da Liverpool, da Manchester City da Manchester United na sha'awar sayen dan gaban Real Madrid na Brazil Rodrygo, kuma za a iya shawo kan kungiyar ta sayar da shi idan ta samu tayin da ya kai na fam miliyan 85 da kari. (Sport)

Liverpool na shirin barin tsohon dan bayan Kamaru Joel Matip, da tsohon dan wasan tsakiya na Sifaniya Thiago Alcantara, da golan Sifaniya Adrian, su bar kungiyar a bazaran nan. (Football Insider)

Fatan Getafe na ci gaba da aron Mason Greenwood, a kaka mai zuwa na neman shiga matsala saboda Manchester United na son sai dai kungiyar ta Sifaniya ta saye shi gaba daya. (Sun)

A shirye Barcelona take ta bai wa Everton 'yan wasa hudu wadanda suka hada da Ansu Fati, da Clement Lenglet, da Sergino Dest da kuma Fermin Lopez - domin kawai kungiyar ta Ingila ta yarda ta sayar mata da dan wasan tsakiya Amadou Onana na Senegal wanda aka yi wa kudi fam miliyan 80. (Sport via Teamtalk)

Dan wasan tsakiya na Netherlands Teun Koopmeiners ya gaya wa kungiyarsa ta Italiya cewa yana son tafiya a bazaran nan, inda ake alakanta shi da Liverpool. (Metro)

Aikin kociyan Manchester United Erik ten Hag ba ya cikin hadari a ragowar kakan nan bayan da ya burge sabon mai kungiyar Sir Jim Ratcliffe a farko-farkon lokacin da sabon kungiyar ya saye ta. (Guardian)

dan gaban Jamus Timo Werner, na son sauya zaman aron da yake yi a RB Leipzig zuwa zaman dindindin a Tottenham Hotspur abin da zai iya sa kungiyar ta saye shi kasa da fam miliyan 15. (Telegraph)

Kungiyoyin Saudiyya na matukan son tsohon dan gaban Arsenal da Faransa Alexandre Lacazette kuma kyaftin din na Lyon ka iya zama wani tauraro na Turai da zai tafi Saudiyya a karshen kakar nan. (L'Equipe)

AC Milan za ta nemi sakin Divock Origi, idan tsohon dan wasan na Liverpool ya koma daga aron da ta bayar da shi a Nottingham Forest.(Calciomercato )

Roy Keane ya ce yana ganin hakan ka iya faruwa lokacin da aka yi masa maganar yuwuwar kociyan Ingila tafiya Manchester United. (Sky Sports)

Newcastle na sa ido a kandan bayan Feyenoord da Netherlands Quilindschy Hartman, a kokarin da kungiyar take yi na kara karfi. (Football Transfers)

Dan bayan Manchester United da Sweden Victor Lindelof, ya ce zai mayar da hankalinsa ne a kan zamansa da Manchester United amma ba tafiya Saudiyya ba. (Fotbollskanalen)