'Yan Real Madrid 14 aka gayyata tawagoginsu buga wasanni

An wallafa

Kimanin 'yan Real Madrid 14 ne aka gayyata tawagoginsu, domin buga wasannin sada zumunda har da Lunin mai fatan samun gurbin shiga Euro 2024.

A karshen makon nan ba wasannin lik a fadin duniya, inda Fifa kan ware lokacin buga ko dai wasan sada zumunta ko na neman shiga gasar kofin duniya ko na Turai da sauransu.

Real Madrid wadda saura wasa tara ta kammala La Liga na shekarar nan tana ta daya a kan teburi da tazarar maki takwas tskani da Barcelona ta biyu.

Cikin 'yan Real da aka gayyata sun hada da Carvajal da Joselu da Brahim da Rüdiger da Kroos da Camavinga da chouameni da Bellingham da Modrić da Arda Güler da Valverde da Vini Jr da Rodrygo da kuma Lunin

Sifaniya - Wasan sada zumunta

Sifaniya da Colombia (Juma'a 22 ga watan Maris)

Sifaniya da Brazil (Talata 26 ga watan Maris)

Carvajal da Joselu za su buga wa Sifaniya wasan sada zumunta biyu da za ta buga.

Za ta yi wasan farko a Landan da Colombia, sannan ta kara na biyu a filin wasan Real Madrid wato Santiago Bernabéu da Brazil mai dauke da Vini Jr. da kuma Rodrygo.

Ukraine - Wasan neman tikitin shiga Euro 2024 Ukraine

Bosnia and Herzegovina da Ukraine (Alhamis 21 ga watan Maris)

Ukraine ta kira Lunin domin ya buga mata wasannin cike gurbin shiga Euro 2024.

Za ta fara wasa da Bosnia and Herzegovina, idan ta kai bantenta za ta kece raini a wasan gaba ranar Talata 26 ga watan Maris da wadda ta yi nasara tsakanin Israel ko kuma Iceland.

Faransa - Wasan sada zumunta

Faransa da Jamus (Asabar 23 ga watan Maris)

Faransa da Chile (Talata 26 ga watan Maris)

Camavinga da Tchouameni za su buga wa Faransa wasan sada zumunta biyu a gida.

Za su fara fafatawa da Jamus a Lyon, sannan wasa na biyu da Chile a Marseille.

Ingila - Wasan sada zumunta

Ingila da Brazil (Asabar 23 ga watan Maris)

Ingila da Belgium (Talata 26 ga watan Maris)

Ingila ta gayyaci Jude Bellingham domin ya buga mata wasan sada zumunta biyu da za ta kara a Wembley.

Za ta fara fuskantar Brazil mai dauke da 'yan wasan Real Madrid, Vinicius Jr da kuma Rodrygo, sannan ta buga na biyu da Belgium.

Jamus - Wasan sada zumunta

Faransa da Jamus (Asabar 23 ga watan Maris)

Jamus da Netherlands (Talata 26 ga watan Maris)

Rüdiger da Kroos, wanda zai koma buga wa kasarsa wasanni, an kira shi wasan sada zumunta biyu.

Za ta fara zuwa Faransa mai dauke da 'yan kwallon Real Madrid, Camavinga da Tchouameni, sannan ta yi fafatawa ta biyu da Netherlands.

Brazil - Wasan sada zumunta

Ingila da Brazil (Asabar 23 ga watan Maris)

Sifaniya-Brazil (Talata 26 ga watan Maris)

Vini Jr. da Rodrygo za su buga wasa biyu na sada zumunta da kasashen da ke dauke da 'yan kwallon Real Madrid.

Na farko da Ingila mai Jude Bellingham a Wembley, sannan su fuskanci Carvajal da Joselu a tawagar Sifaniya da za su kece raini a Santiago Bernabéu..

Croatia - Wasan sada zumunta

Tunisia-Croatia (Asabar 23 ga watan Maris)

Modrić ne zai yi wa Croatia kyaftin a wasannin sada zumunta na lashe kofi a Masar.

Za su kara da Tunisia a zagayen daf da karshe a Air Defence Stadium.

Sannan fafatawar gaba ko dai matakin neman na uku ko kuma wasan karshe.

Haka kuma Croatia za ta kara da New Zealand ranar Talata 26 ga watan Maris.

Turkiya - Wasan sada zumunta

Hungary da Turkiya (Juma'a 22 ga watan Maris)

Austria da Turkiya (Talata 26 ga watan Maris)

Dan kwallon Real Madrid, Arda Güler zai yi wa Turkiya wasan sada zumunta biyu a gida da za ta kara da Hungary da kuma Austria.

Morocco - Wasan sada zumunta

Morocco da Angola (Juma'a 22 ga watan Maris)

Morocco da Mauritania (Talata 26 ga watan Maris)

Brahim zai wakilci Morocco a karon farko a fafatawa biyu da za ta yi a wasan sada zumunta a gida a filin wasa da ke Agadir da za ta fuskanci Angola da kuma Mauritania.

Uruguay - Wasan sada zumunta

Euskadi da Uruguay (Asabar 23 ga watan Maris)

Uruguay da Ivory Coast (Tuesday 26 ga watan Maris)

Valverde zai yi wasan sada zumunta biyu a Turai, wanda na farko a Bilbao da Euskadi, sannan ta buga na biyu a Lens da Ivory Coast.