Yadda ƴan bindiga ke tilasta wa mutane yin hijira a Sokoto

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Mazauna yankin sun ce an ƴanbindigar sun kashe mutane da garkuwa da wasu sa sace shanu da kuma tilasta wa mutane da dama yin gudun hijira.

Al'ummar garuruwan Dinawa da Achida da Saketa da Manuna da Caco sun ce hare-haren da ƴanbindigar sun zama wani abu da ke faruwa kusan kullum.

Wani mutumin garin Dinawa ya ce mahaifinsa na cikin waɗanda ƴanbindigar suka kashe a baya-bayan nan.

''Muna cikin tashin hankali da ɗimuwa da hirgici, jiya ma sai da suka shiga garin Manuna suka kashe ɗa da uba da mace guda huɗu. Haka kuma a garinmu na Dinawa, ni kaina sun kashe mun mahaifi.'' In ji shi.

Ya ƙara da cewa ''Yanzu kowacce rana ta Allah, wannan ƙaramar hukuma ta Wurno in sun shiga wannan gari yau, gobe sai su shiga wani. Sun mayar da abin kamar cin kasuwa.

''Ba mu bar garin ba amma da an ce ma ƙarfe shida ta yi na marece, to kowa ya kama gaba nai. Za ka ga wasu suna komawa ƙaramar hukumar Wurno wasu za su je Achida wasu kuma za su je Sokoto don ba a kwana a garin.''

Shi ma wani mazauni garin Achida a karamar hukumar ta Wurno ya ce mutane da dama ne ke gudun hijira sakamakon hare-haren na yanbindiga

''Al'umma gasu nan suna ketowa aƙalla za ka ga mai tirela ya kwaso mutum dam, kamar za su je cirani Kudu. Ba kowa bane ƴan gudun hijira za a aje mana su Achida kuma dole ka ga tattalin arzikinmu ba mu iya ɗaukar nauyin su saboda halin da ak ciki na rayuwa.'' In ji shi.

Ya ce ƴan gudun hijirar da ke tururuwa Achida ''suna fitowa ne daga yankunan Caco, Dinawa kuma ita hanyar Caco ma ta koma kamar Sambisa, da ance ma ƙarfe biyar ta yi kayi kaɗan ka bi. Ka ga kuwa bai kai kilomita huɗu zuwa biyar ba daga Achido.''

Al'ummomin dai sun buƙaci hukumomi su kawo masu ɗauki tare da tallafi, domin samun sauƙin halin da suke ciki.

BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin hukumomin jihar Sokoto a kan wannan batu, amma hakan ba ta samu ba.

jihar Sokoto dai na ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren ƴan fashin daji da ke satar mutane domin neman kuɗin fansa, kuma matsalar na ci gaba da kamari duk da ƙoƙarin da jami'an tsaro ke cewa suan yi wajen kawar da ita.