Newcastle ta kasa hawa kan teburin Premier a makon nan

Asalin hoton, Getty Images
Fulham ta kawo karshen wasa huɗu da Newcastle ta yi a bana ba tare da an doke ta ba da fara babbar gasar tamaula ta Ingila.
Newcastle ta yi rashin nasara da cin 3-1 a Craven Cottage a wasan mako na biyu a Premier League ranar Asabar.
Fulham ta ci ƙwallayen ta hannun Jiménez da Smith Rowe da kuma ta hannun Nelson, yayin da Newcastle ta zare ɗaya ta hannun Hervey Barnes.
Karon farko da Barnes ya ci ƙwallo a wasa karo na uku kenan a jere sau biyu yana wannan bajintar tun farko a Leicester City a 2020.
Kafin wannan wasan newcastle ta yi nasara hudu a gidan Fulham, wadda kafin nan aka doke ta karawa shida a Craven Cottage.
Karon farko da aka doke Newcastle a bana, wadda ta yi nasara uku da canjaras daya a wasa biyar, Fulham kuwa ta ci wasa na biyu da canjaras biyu aka doke ta karawa daya.
Da wannan sakamakon Newcastle ta koma ta shidan teburi, bayan wasa biyar, yayin da Fulham ta yi sama zuwa mataki na takwas.






