Wolves ta naɗa Vitor Pereira a matsayin sabon kocinta

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Wolves ta naɗa tsohon kocin Porto Vitor Pereira a matsayin sabon kocinta.
Kocin na Portugal ya koma Wolves ne daga Al-Shabab na Saudiyya kan kwantaragin watanni 18, inda Wolves ɗin za ta biya shi kimanin fan 825,000 a matsayin kudin diyya.
Ya maye gurbin tsohon kocinta Gary O'Neil wanda aka kora a ranar Lahadi bayan rashin nasarar da ya yi a ranar Asabar a hannun Ipswich 2-1, wanda hakan ya mayar da ƙungiyar ta biyun ƙarshe a Premier.
A ranar Alhamis Pereira ya fara jan ragamar ƙungiyar a filin atisaye a karon farko ranar Alhamis, kuma zai fara wasa ne da Leicester City da ke matsayi na 17 da banbancin maki biyar tsakaninta da Wolves.
Sai da aka ɗauki lokaci Wolves na neman wanda zai maye gurbinta ciki har da tsohon kocin West Ham David Moyes.
Daga baya aka zaɓi Pereira wanda ya lashe Primeira Lig na Portugal da FC Porto a 2012 da 2013 da kuma Greek Super League da Olympiakos a 2015.
Shi ne ke jan ragamar Al-Shabab ta Saudiyya tun watan Fabirairu kuma ya barsu suna matsayi na shida a teburin gasar Saudi Pro.
Dan shekara 56 ya maye gurbin O'Neil ne da aka ɗauke shi aiki a Molineux a watan Agustan 2023, yayin da Wolves ta yi rashin nasara a wasanni 11 cikin 16 da ta buga a Premier bana.
Wasa biyu kacal suka ci, wanda suka yi da Fulham da kuma Southampton, yayin da tsawon shekaru bakwan da suka kwashe a Premier ke fuskantar barazana.











